Gwamnatin Neja ta bayyana wuraren da Boko Haram ke iko da su a jihar

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Sakataren gwamnatin jihar Neja, Ahmed Matane ya bayyana cewa, ’yan ta’addar Boko Haram sun ƙwace garuruwa biyar a qananan hukumomin Rafi da Shiroto a jihar Neja.

Ya bayyana hakan ne a wata hira da ya yi da Kamfanin Dillancin Labaran Nijeriya a Minna, babban birnin jihar a ranar Litinin.

Ya yi bayanin cewa, mayaƙan na Boko Haram suna da cikakken iko a Hanawanka, Madaka, a ƙaramar hukumar Rafi da Kurebe, Gussau, Farina Kuka a ƙaramar hukumar Shiroro, wanda hakan ya tilasta wa mazauna karkara yin hijira zuwa wasu wurare.

Ya ce, ’yan ta’addan na tafiya cikin walwala a yankunan da abin ya shafa, suna riƙe da nagartattun makamai da kuma muggan makamai.

Matane ya ce, tuni jihar ta sanar da hukumomin tsaro domin ɗaukar matakan tsaro na gaggawa.

Ya qara da cewa, “mun kashe sama da Naira biliyan 2 kan jami’an tsaro wajen yaƙi da ’yan bindiga da garkuwa da mutane da sauran miyagun ayyuka a cikin shekaru biyu da suka wuce. Za mu ci gaba da ba da fifiko ga jin daɗin jami’an tsaron da aka tura domin ba su damar kawar da duk waɗanda ke da hannu a cikin haramtattun ayyuka tada zaune tsaye.”

“Haka zalika, mun yi kira ga mazauna yankin da su ba da gudummawar ingantattun bayanai game da duk wani motsin da ba su gamsu da shi ba zuwa ga ofisoshin tsaro mafi kusa don ɗaukar matakan tsaro. Mun kuma tuntuɓi shugabannin gargajiya da na addini da kuma masu ruwa da tsaki don jawo hankalin jama’a don tallafa wa ƙoƙarin gwamnati a ci gaba da yaƙi da masu aikata laifuka,” inji shi.

Matane, ya kuma yaba tare da yabawa ƙoƙarin gwamnatin jihar Neja na shawo kan matsalar.

Ya ce, gwamnati ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen ganin ta kawo ƙarshen ƙalubalen tsaro da ke addabar Jihar.