Mahara sun tashi bamabamai a birnin Kampala

Daga BASHIR ISAH

Rahotanni daga Kampala babban birnin ƙasar Uganda sun ce, aƙalla mutum uku ne suka mutu sannan wasu da dama sun jikkata sakamakon wani harin da aka kai a birnin ranar Talata.

Mai magana da yawun ‘yan sandan yankin, Fred Enanga ya ce, an kai mutum 33 ya zuwa babban asibitin birnin inda ake yi musu maganin raunukan da suka ji a dalilin harin.

Haka nan, jami’in ya ce wasu ‘yan ƙunar baƙin-wake su uku sun rasa rayukansu a harin. Ya ce fashewa mai ƙarfin gasken da ta auku a birnin ta girgiza jama’a ainun lamarin da ya sanya mazauna yankin tserewa don neman mafaka.

Bayanan ‘yan sandan yankin sun ce fashewa biyu suka auku inda aka samu tazarar mintuna uku tsakanin fashewar farko da ta biyun.

Tare da cewa sun samu nasarar daƙile hari na uku da maharan suka shirya bayan da suka cafke wani da ake zargi da hannu a harin.