02
Feb
Daga WAKILIN MU A safiyar Talata (02/02/2021), wasu da ake zargin 'yan fasa-ƙwauri ne suka kai wa jami'an Hukumar Yaƙi da Fasa-ƙwauri na shiyyar 'Zone A' hari yayin da suke bakin aiki a kan babban hanyar Abeokuta a jihr Ogun. Bayanan da jaridar Manhaja ta samu sun nuna cewa, waɗanda lamarin ya shafa sun yi haka ne domin tirjiya daga kamun jami'an a daidai lokacin da suke ƙoƙarin arcewa da shinkafar ƙetare maƙare cikin motocinsu. Bayanai sun nuna cewa, bayan da jami'an Kwastam suka kama motocin ne sai wasu ɓatagari da ke goyon bayan 'yan fasa-ƙwaurin suka haɗa kansu suka…
