12
Feb
Daga AISHA ASAS Hukumar Yaƙi da Fasa-ƙwauri ta Ƙasa a Jihar Ogun, ta ce wasu 'yan fasa-ƙwauri sun kai wa jami'anta hari a bakin aiki a Larabar da ta gabata inda aka yi musayar wuta wanda hakan ya yi sanadiyar mutuwar wani mazaunin ƙauyen Ohunbe mai suna Tunde Alabe. A cewar hukumar an yi arangamar ne a lokacin da jami'an kwastam suka yi ƙoƙarin daƙile fasa-ƙwaurin fetur zuwa ƙetare da masu harkar suka so yi. Ta ce ɓata-garin sun far wa jami'anta ne ɗauke da muggan makamai da suka haɗa da sanduna da bindigogi da dai makamantansu. Lamarin ya yi…
