26
Feb
Daga AISHA ASAS Ofishin Hukumar Yaƙi da Fasa-ƙwauri ta Nijeriya (NCS) da ke Apapa a Legas, ya ce ya kama wani kwantena mai lamba 1793504 wanda aka yi amannar tais (tiles) ne aka ɗauko, amma bayan da aka zurfafa bincike sai aka gano katan-katan na ƙwayar taramo guda 554 maƙare a cikin sunduƙin. Da yake yi wa manema labarai bayani a ranar Alhamis da ta gabata Shugaban Hukumar na Apapa, Controller Malanta Yusuf, ya ce kimanin makonni uku da kama aiki a Apapa, sun yi nasarar kama sunduƙai da dama ɗauke da kayayyakin da aka haramta shigo da su cikin…
