Kasuwanci

Za a soma aikin gyaran gada a Legas

Za a soma aikin gyaran gada a Legas

Daga FATUHU MUSTAPHA Gwamnatin Tarayya ta bada tabbacin cewa nan bada daɗewa ba, za ta soma aikin gyran gadar hanyar zuwa filin jirgin sama a birnin Legas wadda ta ƙone a lokutan baya. Babban Sakataren Ma'aikatar Ayyuka a Gidaje ta Tarayya, Alhaji Babangida Hussaini, shi ne ya faɗi haka yayin wani rangadi da ya yi a Legas domin duba wasu ayyukan gidaje da hanyoyi da ke gudana a jihar. Gadar da lamarin ya shafa ta ci wata ne sakamakon haɗarin tankar mai da ya auku a Janairun da ya gabata, kuma a wancan lokaci aka rufe gadar aka hana abubuwan…
Read More
Akume ya ƙalubalanci masu gidajen caca kan tara wa gwamnati kuɗaɗen shiga

Akume ya ƙalubalanci masu gidajen caca kan tara wa gwamnati kuɗaɗen shiga

Daga WAKILINMU Ministan Ayyuka na Musamman, Sanata George Akume, ya buƙaci Hukumar Kula da Harkokin Caca ta Ƙasa (NRLC) da ta ƙara himma wajen tara wa gwamnati kuɗaɗen shiga domin ƙarfafa mata wajen yi wa ƙasa ayyukan cigaba da inganta tattalin arziki. Akume ya buƙaci hakan daga hukumar ne a Alhamis da ta gabata yayin wata ganawa da masu ruwa da tsaki a masana'antar caca a Abuja. Inda ya ce an rigaya an bai wa hukumar dama don yin abin da ya kamata. Ya ce, "Abin takaici ne ganin yadda ake tafka hasarar ta wannan ɓangare saboda babu abin da…
Read More
Ibadan: EFCC ta gurfanar da dattijo gaban kotu kan zambar kuɗin fili milyan N25

Ibadan: EFCC ta gurfanar da dattijo gaban kotu kan zambar kuɗin fili milyan N25

Daga WAKILINMU Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Zagon Ƙasa da Zambar Kuɗaɗe (EFCC) ta shiyyar Ibadan, ta gurfanar da wani dattijo ɗan shekara 68 a gaban kotu bisa zargin zambar kuɗaɗen fili har naira milyan 25. EFCC ta gurfanar da Ezekiel Oluwadare James a gaban Mai Shari'a Patricia Ajoku ne kan laifuka guda biyu, wato haɗin baki da kuma samun kuɗi ba ta hanyar da ta dace ba. Wanda a cewar hukumar hakan ya saɓa wa sashe na 8(a) na dokokin zamba da sauran laifuka masu alaka da haka na 2006, wanda hakan ya cancanci horo a ƙarƙashin…
Read More
WTO: Ba domin Buhari ba da ban kaiblabari ba – Dr Ngozi

WTO: Ba domin Buhari ba da ban kaiblabari ba – Dr Ngozi

Daga FATUHU MUSTAPHA Shugabar Hukumar Cinikayya ta Duniya, Dr. Ngozi Okonjo-Iwela, ta ce taimako da goyon bayan da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi mata sun yi matuƙar tasiri wajen ba ta nasarar ɗarewa kujerar jagorancin hukumar WTO. Ngozi ta bayyana haka ne a lokacin da ta kai wa Buhari ziyara don nuna godiyarta, tana mai cewa zaɓin da Buhari ya yi mata wajen tsayawa takara da ɗaruruwan wasiƙun da ya rubuta wa shugabannin duniya da kiran da ya yi musu ta waya domin goya mata baya sun taimaka mata wajen samun nasara. Ta ci gaba da cewa da ba…
Read More
IPMAN ta bada umarnin ci gaba da sayar da fetur kan N163

IPMAN ta bada umarnin ci gaba da sayar da fetur kan N163

Daga FATUHU MUSTAPHA Ƙungiyar 'Yan Kasuwar Fetur Masu Zaman Kansu ta Nijeriya (IPMAN), ta ce ba ta samu wata sanarwar ƙarin kuɗin fetur a hukumance ba, don haka ta buƙaci mambobinta da su yi watsi da jita-jitar da ake ta yaɗawa game da ƙarin farashin fetur. A wata ganawa da ya yi da manema labarai a wannan Juma'ar, shugaban IPMAN reshen jihar Kano, Bashir Dan-Malam, ya bai wa mambobinsu umarnin su ci gaba da saida fetur kan farashin N163 kowace lita. Yana mai cewa duk lokacin da aka samu ƙarin farashin mai a ƙasa, masu ruwa da tsaki na fannin…
Read More
‘Yan sanda sun ceci motocin BRT a Legas

‘Yan sanda sun ceci motocin BRT a Legas

Daga WAKILINMU Rundunar 'yan sanda a Legas, ta ce ta yi nasarar daƙile harkokin ɓatagarin da suka yi yinƙurin yi wa fasinjoji fashi a dogayen motocin safa na BRT a lokacin da aka samu tsaikon abubuwan hawa sakamakon wani haɗari da ya auku. A cewar sanarwar da ta fito ta hannun jami'in hulɗa da jama'a na 'yan sandan jihar, CSP Olumuyiwa Adejobi, ganin abin da ke faruwa sai kwamishinan 'yan sandan jihar, CP Hakeem Odumosu ya bai wa jami'an sashen kai ɗaukin gaggawa (RRS) na rundunar umarnin su je su tabbatar da lumana a yankin da lamarin ya shafa. Daga…
Read More
Ogun: Kwastam ta kama shinkafar ƙetare buhu 5,931, tabar wiwi buhu 290

Ogun: Kwastam ta kama shinkafar ƙetare buhu 5,931, tabar wiwi buhu 290

Daga WAKILINMU A matsayin wani mataki na ci gaba da kare rayuwar matasa daga barin faɗawa garari, Hukumar Yaƙi da Fasa-ƙwauri ta shiyyar Ogon I ta matse ƙaimi wajen yaƙi da fasa-ƙwaurin miyagun ƙwayoyi da sauran kayayyakin da aka haramta shigo da su cikin ƙasa. Da wannan ne hukumar kwastam ɗin ta ce lallai aikin haɗin gwiwar da suke yi tare da Hukumar Yaƙi da Sha da Safarar Muggan Ƙwayoyi (NDLEA) a shiyyar Ogun ya haifar da ɗa mai ido. A cewar shugaban hukumar kwastam na shiyyar, Comptroller PC Kolo, sun samu nasarar kama tabar wiwi har buhu 290 da…
Read More
Kwastam ta kama kayayyakin fasa-ƙwauri na sama da milyan N66

Kwastam ta kama kayayyakin fasa-ƙwauri na sama da milyan N66

Daga AISHA ASAS A ci gaba da yaƙi da harkokin fasa-ƙwauri da take yi, Hukumar Yaƙi da Fasa-ƙwauri ta Ƙasa a shiyya ta biyu (ZONE B) mai hedikwata a Kaduna, ta kama tarin haramtattun kayayyaki daga sassa daban-daban a shiyyar waɗanda a ƙiyasce kuɗinsu ya kai naira milyan N66,133,892.00. Shugaban hukumar a shiyyar 'Zone B' Comptroller AB Hamisu psc(+) shi ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai da suka gudanar a Larabar da ta gabata, tare da nuna kayayyakin da suka kama ga manema labaran. Hamisu ya ce, kayayyakin da suka kama har da wuƙaƙe guda 180 a yankin…
Read More
Legas: Hukumar Kwastam ta kama taramo katan 554

Legas: Hukumar Kwastam ta kama taramo katan 554

Daga AISHA ASAS Ofishin Hukumar Yaƙi da Fasa-ƙwauri ta Nijeriya (NCS) da ke Apapa a Legas, ya ce ya kama wani kwantena mai lamba 1793504 wanda aka yi amannar tais (tiles) ne aka ɗauko, amma bayan da aka zurfafa bincike sai aka gano katan-katan na ƙwayar taramo guda 554 maƙare a cikin sunduƙin. Da yake yi wa manema labarai bayani a ranar Alhamis da ta gabata Shugaban Hukumar na Apapa, Controller Malanta Yusuf, ya ce kimanin makonni uku da kama aiki a Apapa, sun yi nasarar kama sunduƙai da dama ɗauke da kayayyakin da aka haramta shigo da su cikin…
Read More