Kasuwanci

Majalisa ta gayyaci tsohon shugaban FMBN kan badaƙalar kwangilar bilyan N3

Daga AISHA ASAS Majalisar Dattawa ta hannun kwamitinta mai bin diddigin ayyukan gwamnati (SPAC), ta kirayi tsohon shugaban Bankin Bada Bashi (FMBN), Malam Gimba Yau Kumo, da ya bayyana a gabanta kan badaƙalar kwangilar Naira bilyan N3 da aka bayar. Kamar yadda rahoton da aka miƙa wa Ofishin Babban Jami'in Bincike na Ƙasa ya nuna, an bayar da kwangilar ne rukuni-rukuni har huɗu wanda hakan ya yi sanadiyar biyan kuɗi wuce abin da ya kamata a biya da Naira milyan N118,717,892. Bayanan Odita Janar wanda Shugaban Kwamitin Majalisar, Sanata Mathew Urhoghide (PDP Edo ta Kudu), ya bayyana wa manema labarai…
Read More
Duk dillalin da ya ƙara farashin kayayyaki a bakin lasisinsa – BUA

Duk dillalin da ya ƙara farashin kayayyaki a bakin lasisinsa – BUA

Daga FATUHU MUSTAPHA Shugaban rukunin kamfanonin BUA, Alhaji Abdulsamad Isyaku Rabiu, ya yi barazanar ƙwace lasisin duk wani dillalin kamfanin da aka kama ya tsawwala farashin kayayyaki yayin watan Ramadan. Alhaji Abdulsamad Rabiu ya bai wa al'umma tabbacin kamfaninsa ya tanadi wadatattun kayayyakin masarufin da za su ishi ɗaukacin jihohin ƙasar nan a lokacin Ramadan da kuma bayansa da zummar hana faruwar matsin da 'yan ƙasa kan fuskanta da zarar watan Ramadan ya kama. Shugaban BUA ya bayyana haka ne ta bakin wakilinsa na yankin Arewa, Alhaji Mohammad Adakawa, yayin wata ganawa da ya yi da manema labarai a Kano.…
Read More
Rundunar JBPT ta kama haramtattun kayayyaki na N61

Rundunar JBPT ta kama haramtattun kayayyaki na N61

Daga AISHA ASAS A ci gaba da yaƙi da harkar fasa-ƙwauri da take yi a sassan ƙasa, Rundunar Haɗin Gwiwa ta Joint Border Patrol Team (JBPT) rukuni na 3 a jihar Kwara, a cikin makonni 3 ta fatattaki 'yan fasa-ƙwauri tare da ƙwace tarin kayayyaki wanda a ƙiyasce kuɗinsu ya kai Naira milyan N61. Kazalika, randunar ta samu nasarar daƙile wasu baƙin haure masu shiga ƙasa ba a bisa tsarin da doka ta shimfiɗa ba. Daga cikin tarin kayayyakin da rundunar ta kama, har da shinkafar ƙetare buhu 1,274, motoci tokumbo guda 23, ƙaramar bindiga ƙirar gida da alburusai guda…
Read More
NAFDAC ta gargaɗi ‘yan Nijeriya kan amfani da jabun shayi

NAFDAC ta gargaɗi ‘yan Nijeriya kan amfani da jabun shayi

Daga WAKILINMU Hukumar Kula da Ingancin Abinci da Magunguna (NAFDAC), ta yi jan hankali ga 'yan Najeriya game da wani jabun shayi da ake sayarwa wanda aka ce yana maganin ciwon sukari. Hukumar ta gargaɗi 'yan nijeriya da su guji yin amfani da 'insulin tea' wanda ko rajista bai da shi balle kuma ingancin warkar da wata cuta. Shugabar NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye ce ta yi wannan gargaɗi a wata sanarwar manema labarai da ta fitar a Lahadin da ta gabata a Abuja. Adeyeye ta buƙaci duk inda aka ga ana sayar da wannan shayi na 'insulin tea' a gaggauta…
Read More
CBN ya bai wa DisCos bilyan N33.4 don aikin rarraba mita, inji NERC

CBN ya bai wa DisCos bilyan N33.4 don aikin rarraba mita, inji NERC

Daga FATUHU MUSTAPHA Kawo yanzu, Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya bai wa Kamfanonin Rarraba Lantarki (DisCos) kuɗi Naira bilyan N33.4 daga cikin bilyan N59.2 da aka ware musamman domin aikin raba mita ga 'yan Nijeriya na Gwamnatin Tarayya, in ji Hukumar Kula da Wutar Lantarki ta Nijeriya (NERC). Shugaban NERC, Engr Sanusi Garba ne ya bayyana haka yayin wata ganawa tsakanin Kwamitin Majalisar Dattawa kan Sha'anin Lantariki da jami'an NERC da kuma wakilan DisCos, kwanan nan a Abuja. Garba ya ce shirin raba mitar wanda ake sa ran gidaje miliyan guda su ci moriyarsa a faɗin ƙasa tsakanin Oktoban 2020…
Read More
Gwamnati na shirin kashe tiriliyan N1 don gina masana’antu a ƙananan hukumomi 774

Gwamnati na shirin kashe tiriliyan N1 don gina masana’antu a ƙananan hukumomi 774

Daga FATUHU MUSTAPHA Gwamnatin Tarayya ta gabatar da ƙudirin ƙirƙiro da masana'antar cikin gida guda ɗaya a kowace ƙaramar hukuma daga ƙananan hukumomi 774 da ake da su a ƙasar nan. Gwamnatin ta ce tana sa ran kashe kuɗi naira tiriliyan N1 ne domin cim ma wannan ƙudiri. Ministan Ayyuka na Musamman, Sanata George Akume ne ya bayyana hakan yayin ganawarsu da Kwamitin Majalisar Dattawa Kan Ayyuka na Musamman. Inda ya ce irin wannan masana'anta ta cikin gida za ta maida hankali ne wajen samar da kayayyakin masarufi don amfanin al'ummar yankin da aka kafa masana'antar a cikinta. Da yake…
Read More
Majalisa za ta binciki yadda aka kashe Dala bilyan $1.5 wajen gyaran matatar mai a Fatakwal

Majalisa za ta binciki yadda aka kashe Dala bilyan $1.5 wajen gyaran matatar mai a Fatakwal

Daga UMAR M. GOMBE Majalisar Wakilai ta Ƙasa ta umarci kwamitinta mai sanya ido kan albarkatun man fetur da ya gudanar da bincike domin sanin haƙiƙanin gaskiyar lamari game da matatar mai na Fatakwal wadda Gwamnatin Tarayya ta ware zunzurutun kuɗi har Dala bilyan $1.5 domin aikin gyaran matatar. Kazalika, majalisar ta farlanta wa kwamitin gudanar da bincike kan kuɗaɗen da aka kashe a baya wajen gyaran matatar mai na Fatakwal da sauran matatun mai da ake da su a faɗin ƙasa. Ɗaukar wannan mataki ya faru ne biyo bayan ƙorafin da ɗan majalisa Onofiok Luke, na jam'iyyar PDP daga…
Read More
Attah ya yi ƙarin haske kan batun biyan harajin sayen jiragen sama

Attah ya yi ƙarin haske kan batun biyan harajin sayen jiragen sama

Daga AISHA ASAS Hukumar Yaƙi da Fasa-ƙwauri ta Ƙasa ta yi ƙarin haske tare da kore raɗe-raɗin da aka yi ta yaɗawa kan batun biyan harajin VAT da Kwastam Duti kan sayen jiragen sama da sauran kayayyakin jiragen. Idan dai za a iya tunawa, wasu kafafen yaɗa labarai sun ruwaito Shugaban Air Peace Airline na cewa har yanzu Hukumar Kwastam na karɓar harjin Duti da na VAT duk da umarnin hani ga hakan da Gwamnatin Tarayya ta gindaya wanda a cewarsa hakan na maida wa kamfanonin sufurin jiragen sama hannun agogo a baya. Sai dai mai magana da yawun hukumar…
Read More
Kuɗin makamai: Majalisar Wakilai ta gayyaci Attahiru da Emefiele

Kuɗin makamai: Majalisar Wakilai ta gayyaci Attahiru da Emefiele

Daga FATUHU MUSTAPHA Majalisar Wakilai ta Ƙasa ta buƙaci Hafsan Hafsoshi, Lieutenant General Ibrahim Attahiru da Gwamnan Babban Bankin Nijeriya (CBN), Godwin Emefiele, da su bayyana a gaban wani kwamitinta ya zuwa watan gobe. Kwamitin Majalisar ƙarƙashin shugabancin Hon Olaide Akinremi, ya gayyaci waɗanda lamarin ya shafa ne a Litinin da ta gabata bayan da suka ƙi amsa masa gayyatar farko da ya yi musu. Hon Bede Eke shi ne wanda ya gabatar da ƙudirin a gayyato mutum biyun zuwa gaban Majalisar, wanda ya nuna ɓacin ransa kan rashin amsa gayyatar kwamitin majalisar a baya. 'Yan majalisar mambobi ne a…
Read More
Kwastam ta kama shinkafar ƙetare buhu 905 a cikin makonni biyu

Kwastam ta kama shinkafar ƙetare buhu 905 a cikin makonni biyu

Daga AISHA ASAS Hukumar Yaƙi da Fasa-ƙwauri ta Nijeriya ta 'Zone B' a Kaduna, ta baje kolin tarin kayayyakin da ta kama an yi fasa-ƙwaurinsu a tsakanin makonni biyu, a Maris. A cewar Comptroller Al-Bashir Hamisu, sun samu nasarar kama waɗannan kayayyaki ne a wurare daban-daban a shiyyar. Daga cikin kayayyakin da hukumar ta ce ta kama har da shinkafar ƙetare buhu 905 da man girki jarka 541 da dila 138 na gwanjon sutura da motoci guda 6 da dai sauransu. Ga baki ɗaya, hukumar ta ce harajin da ya kamata a biya a kan waɗannan kayayyaki ya kai naira…
Read More