Majalisa za ta binciki yadda aka kashe Dala bilyan $1.5 wajen gyaran matatar mai a Fatakwal

Daga UMAR M. GOMBE

Majalisar Wakilai ta Ƙasa ta umarci kwamitinta mai sanya ido kan albarkatun man fetur da ya gudanar da bincike domin sanin haƙiƙanin gaskiyar lamari game da matatar mai na Fatakwal wadda Gwamnatin Tarayya ta ware zunzurutun kuɗi har Dala bilyan $1.5 domin aikin gyaran matatar.

Kazalika, majalisar ta farlanta wa kwamitin gudanar da bincike kan kuɗaɗen da aka kashe a baya wajen gyaran matatar mai na Fatakwal da sauran matatun mai da ake da su a faɗin ƙasa.

Ɗaukar wannan mataki ya faru ne biyo bayan ƙorafin da ɗan majalisa Onofiok Luke, na jam’iyyar PDP daga Akwa Ibom ya gabatar wa majalisar don amfanin al’ummar ƙasa.

‘Yan majalisar sun nuna damuwarsu matuƙa kan yadda suka ce gwamnati ta kashe maƙudan kuɗi wajen gyaran matatun ba tare da samun wani kyakkyawan sakamako ba.

Haka nan, sun buƙaci Gwamnatin Tarayya ta bada lasisi da kuma tallafin da za su bada damar samar da wasu ƙananan matatun mai a ƙasa.

Makonni shida kacal Majalisar ta bai wa kwamitin a kan ya kammala bincikensa tare da gabatar mata da rahotonsa.