JAMB za ta soma sayar da fom na 2021 a Afrilu

Daga FATUHU MUSTAPHA

Hukumar Shirya Jarabawar Shiga Manyan Makarantu (JAMB) ta bada sanarwar ya zuwa ranar 8 ga Afrilu mai zuwa za ta soma gudanar shirin yin rajista na UTME/ Direct Entry (DE) na 2021 a faɗin ƙasa domin amfanin masu neman gurbin karatu a manyan makarantun gaba da sakandare.

A sanarwar da hukumar ta fitar ta hannun mai magana da yawunta, Fabian Benjamin a Abuja, hukumar ta ce ana sa ran kammala shirin yin rajistan ya zuwa 15 ga Mayu.

Yayin wani taro da jagororin hukumar suka gudanar a Talatar da ta gabata, sun cim ma matsayar cewa dole duk ɗalibin da zai yi rajista ya haɗa da Lambar Shaidar Ɗan Ƙasa (NIN).

Tare da cewa, shirin yin rajistar zai gudana ne a cibiyoyin rajista guda 700 da ake da su a ƙasa baki ɗaya.

Ga sharuɗɗan da JAMB da shimfiɗa game da yin rajistar kamar haka:

i. Wajibi ne ɗalibi mai buƙatar yin rajista ƙarƙashin UTME/DE, ya saka Lambar Shaidar Ɗan Ƙasa (NIN) a bayanansa.

ii. Shirin rajistar zai gudana ne a tsakanin cibiyoyi 700 a faɗin ƙasa. Za a iya samun jerin cibiyoyin a ofishin JAMB na jihohi da kuma shafinta na intanet: www.jamb.gov.ng

iii. Ga tsarin yadda shirin rajistar zai gudana:

a. Za a soma yin rajista ranar Alhamis, 8 ga Afrilu sannan a kammala ranar Asabar, 15, Mayu, 2021.

Ɗalibai su sani, rajistar DE za ta gudana tare ne da na UTME. Kuma babu wani ƙarin lokaci na sayar da fom da za a yi.

b. Za a yi gwajin sharar fage (Optional Mock) a ranar Juma’a, 30, Afrilu, 2021 (ga waɗanda ke da sha’awar haka, sannan su tabbatar sun yi rajista kafin 24, Afrilu, 2021).

c. Tsakanin Asabar, 5 zuwa Asabar, 19 ga Yuni, 2021 ne za a gudanar da jarabawar bai ɗaya.

iiii. Cibiyar da za a rubuta jarabawa za ta kasance a nan garin da ɗalibi ya zaɓi ya rubuta jarabawarsa.

v. Kuɗin rajista N3,500 ne, sai kuma N500 na abin karatu da aka bada shawarar a mallaka.

vi. Za a yaɗa sauran bayanai game da shirin rajistar a shafin intanet na hukumar da kuma kafafen yaɗa labarai daga kan 5 ga Afrilu, 2021.