04
Jun
Daga UMAR M. GOMBE Jami'an Hukumar Yaƙi da Fasaƙwauri ta Nijeriya, sun yi nasarar kama kayayyakin fasaƙwauri da harajinsu ya kai milyan N101,027,350 wanɗanda aka shigo da su cikin ƙasa ta ɓarauniyar hanya a jihar Kastina. Daga cikin kayayyakin da jami'an suka kama a ranar Alhamis da ta gabata har da motoci guda 14 da harajinsu ya kai milyan N91,592,500, haɗa da kayan abinci da sauransu waɗanda harajinsu ya kai N9,434,850. Da yake bayani yayin taron manema labarai a babban ofishin hukumar na yankin Katsina, Shugaban Riƙo na Kwastam na Katsina, DC Dalha Wada Chedi, ya jaddada aniyar Hukumar Kwastam…
