Kwastam ta kama haramtattun kayayyaki na bilyan N3.1 a Legas

Daga FATUHU MUSTAPHA

Hukumar Yaƙi da Fasa-ƙwauri na shiyyar Zone A a birnin Legas, ta kama durom 42 maƙare da tokar bindiga (calcium carbide) wanda aka shigo da su cikin ƙasa a sace daga ƙasar Benin.

Masana sun yi gargaɗin cewa lamarin fa ba zai yi daɗi ba idan irin wannan makamashi ya faɗa a hannu ɓata-gari.

Hukumar Kwastam ta ce makamashin abu ne da za a iya amfani da shi wajen haɗa abubuwa masu fashewa masu ƙarfin tarwatsa gine-gine.

Shugaban riƙo na hukumar a Zone A, Compt. Usman Yahaya, ya shaida wa manema labarai cewa baya ga tokar bindigar da suka kama, sun kuma cafke kayayyaki da dama waɗanda aka haramta shigo da su cikin ƙasa wanda a ƙiyasce kuɗinsu ya kai milyan N242.

Yahaya ya ce dokar tsarin aikin kwastam (CEMA) sashe na 158 da 147 sun bai wa jami’ansu damar gudanar da aiki tare da shiga gidaje don gudanar da bincike muddin buƙatar hakan ta taso.

Ya ce, “Mun kama tokar bindiga durom 42 biyo bayan bayanan sirrin da muka samu. An yi jigilar kayan ne cikin wata babbar motar ɗaukar kaya inda aka lulluɓe kayan da rogo domin ɓadda sawu wanda a tunaninsu ba za a iya gano su ba.”

Jami’in ya ce sun kama kayan ne a yankin Sango – Ota, ya ce suna da masaniya kan cewa daga ƙasar Benin aka shigo da su. Ya vi gaba da cewa nauyin makamashin ya kai 106KG, sannan harajin da ya kamata a biya a kan kayan ya milyan N105.

Sauran kayayyakin da hukumar ta ce ta kama sun haɗa da; manyan jarka ɗauke da fetur, buhuhunan shinkafar ƙetare, tabar wiwi, ƙwayar taramol, gwanjon tufafi da dai sauransu.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *