Gwamna Abiodun ya roƙi JUSUN ta janye yajin aikin da take yi

Daga UMAR M. GOMBE

Gwamnan Jihar Ogun, Dapo Abiodun, ya yi kira ga Ƙungiyar Ma’aikatan Fannin Shari’a ta Ƙasa (JUSUN) da ta duba sannan ta janye yajin aikin da ta tsunduma tun 6 ga Afrilu, 2021.

Idan dai za a iya tunawa, mambobin JUSUN sun shiga yajin aikin gama gari ne domin neman a aiwatar da cin gashin kai ga fannin shari’a game da sarrafa kuɗaɗe kamar yadda kudin tsarin mulki ya amince da shi.

Gwamnan ya yi wannan kira ne a lokacin da shugabannin JUSUN reshen jihar Ogun suka ziyarce shi a fadar gwamnatin jihar ƙarkashin jagorancin Mr Afolabi Fashanu.

Gwamnan ya ce shi dai yana tare ra’ayin ƙungiyarsu ta gwamnoni kan wannan batu. Daga nan ya yaba tsarin da ‘yan JUSUN ɗin suka bi wajen neman cim ma buƙatarsu.

Jagoran tawagar lauyoyi a yayin ziyarar, Afolabi Fashanu, ya yaba wa gwamnan bisa ƙokarin da yake yi wajen inganta fannin shari’ar jihar. Tare da bai wa gwamnan tabbacin cewa shi da mambobinsu za su san yadda za su yi wajen bai wa JUSUN baki don su fahimci gwamnatin jihar.