Sufeto Janar ya bada umarnin janye manyan jami’an ‘yan sanda daga EFCC

Daga UMAR M. GOMBE

Shugaban Riƙo na Rundunar ‘Yan Sanda na Ƙasa, Usman Baba, ya bada umarnin janye manyan jami’an ‘yan sanda da aka tura aiki a Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Zagon Ƙasa da Zambar Kuɗaɗe (EFCC).

Umarnin na ƙunshe ne cikin wata wasiƙa mai ɗauke da kwanan wata 15, Afrilu, 2021 wadda Usman Baba ya aike wa shugaban EFCC, Abdulrasheed Bawa.

Wasiƙar wadda ta samu sa hannun Idowu Owohunwa babban jami’i na rundunar, ta nuna manyan jami’an ‘yan sanda daga kan muƙamin CSP da aka tura aiki a EFCC, ana buƙatar su koma babban ofishin rundunar da ke Abuja daga ranar Laraba.

Wasiƙar ta ce ɗaukar wannan mataki na janye manyan jami’an daga EFCC, ya yi daidai da tsarin aikin da sabuwar dokar ‘yan sanda ta buƙata.

Sashen wasikar ya nuna cewa, “Na yi wannan wasiƙa ce domin isar da gaisuwar Babban Sufeton ‘Yan Sanda a gare ka tare da sanar da kai cewa Sufeton ya bada umarnin janye duka manyan jami’an da ke aiki tare da hukumarka daga kan muƙamin CSP zuwa sama.

“Da wannan ake buƙatar ka saki dukkan jami’an da lamarin ya shafa domin su gabatar da kansu a babban ofishin rundunar.

“Kazalika, muna buƙatar ka haɗa mana jerin sunayen adadin ‘yan sandan da ke aiki da EFCC, muƙamin kowannensu da kuma ranar tiransfa ɗinsa domin samun damar kimtsa bayananmu.”

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *