Safarar Ƙwayoyi: NDLEA ta kama ƙosai da aka yi da wiwi a oyo

Daga UMAR M. GOMBE

Hukumar Yaƙi da Tu’ammali da Miyagun Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA) reshen jihar Oyo, ta kama tabar wiwi da aka sarrafa shi kamar ƙosai don ɓadda kama a babbar hanyar Legas zuwa Ibadan da ke jihar.

Shugabar NDLEA a jihar Oyo, Mrs Josephine Obi, ita ce ta bayyana haka ga Kamfanin Dillancin Labarai na Nijeriya (NAN) a Ibadan a Talatar da ta gabata.

Haka nan, shugabar ta ce sun cafke wani ɗan aike ɗauke da kek ɗin bikin ranar haihuwa wanda aka cusa tabar wiwi mai nauyin 1.2kg a cikinsa.

Ta ce hanyoyi da dabarun da masu safarar miyagun ƙwayoyi ke amfani da su wajen gudanar da harkokinsu sai ƙaruwa suke kulli yaumi a jijohin ƙasar nan.

A cewarta, “Yadda matasa suka rungumi harkar sarrafa tabar wiwi cikin abinci abin damuwa ne matuƙa, don kuwa abin da NDLEA ta gano yana aukuwa kenan a wasu jijohin ƙasar nan.

“Sukan yi amfani da wasu kayayyaki dangin wiwi ne da giya da sauran ƙwalama irin madara, sukari da sauransu wajen haɗa irin wannan cimar.

“Kuma tuni irin abincin ya shiga manyan shaguna na zamani, wuraren shaƙatawa da kuma makarantu, wanda haka ke jefa yara cikin hali mara kyau.”

A ƙarshe, Obi ta buƙaci al’ummar jihar Oyo su bai wa NDLEA haɗin kan da take buƙata don ba ta damar aiwatar da aikinta a jihar yadda ya kamata.