Jami’an EFCC sun sabunta rantsuwar aiki

Daga FATUHU MUSTAPHA

A matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin da take yi wajen gyara zamanta, Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziki Zagon Ƙasa da Zambar Kuɗaɗe (EFCC), ta bai wa jami’anta damar sabunta rantsuwar aiki a Abuja a Talatar da ta gabata.

Yayin shan rantsuwar, jami’an su yi alƙawarin za su yi aiki da gaskiya ba tare da ha’inci ba.

Shugaban hukumar, Abdulrasheed Bawa, shi ne wanda ya jagoranci shan rantsuwar da ma’aikatan suka yi daidai da dokar aiki ta hukumar.

Bawa

Bayanan sashen yaɗa labarai da hulɗa da jama’a na hukumar suna nuna taron shan rantsuwar ya gudana ne a babban ofishin hukumar da ke birnin tarayya, Abuja.

EFCC ta wallafa a shafinta na twita hotunan taron shan rantsuwar jami’an nata, ciki har da shugabanta Abdulrasheed Bawa wanda ya jagoranci taron.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *