Gwamnatin Tarayya ta sa baki kan rikicin El-Rufai da NLC

Daga AISHA ASAS

Gwamnatin Tarayya ta sa baki cikin rashin jituwan da ke gudana tsakanin gwamnatin jihar Kaduna da ƙungiyoyin ƙwadago na ƙasa.

Ƙungiyar Ƙwadagon ta Ƙasa (NLC) reshen jihar Kaduns da takwararta TUC sun shiga yajin aiki ne na kwanaki biyar da kuma zanga-zanga kan sallamar ma’aikata 7,000 da gwamnatin Kaduna ta yi.

A jawabin da ya yi a madadin Gwamnatin Tarayya a Talatar da ta gabata, Ministan Ƙwadago, Chris Ngige, ya yi kira ga ɓangarori biyu da su yi sulhu da juna.

A cewar Ngige, “Mun san abin da ke faruwa a jihar Kaduna. Matsalar ƙwadago ne kuma ya zama yajin aiki.

“Muna roƙon gwamnan Kaduna kada ya ja lamarin inda ba za a iya shawo kansa ba. Haka nan muna kira ga shugabannin ƙwadago da su maida wuƙarsu cikin kube domin samun damar yin sulhu.

Ngige ya ce ma’aikatarsa ta shiga lamarin yanzu kuma tana kira ga ɓangarorin biyu su yi haƙuri su bada damar a yi suluhu.

Ma’aikatar Kwadago ta ƙasa ta yi kira ga dukkan ma’aikata na musamman irin su likitoci da ma’aikatan jinya da sauransu kan kada su shiga yajin aikin.