HOTO: Buhari da wasu sun yi tsayuwar ‘WAZOBIA’

Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari da Shugabar Cibiyar Cinikayya ta Duniya (WTO), Ngozi Okonjo-Iweala, da kuma Shugaban Bankin Bunƙasa Afirka (AFDB), Akinwumi Adesina, sun yi tsayuwar ɗaukar hoto mai zubin ‘WAZOBIA’ yayin babban taron da suka halarta a Farisa babban birnin Faransa inda aka tattauna batun da ya shafi Afirka.

Duk da dai wataƙila shugabannin ba su kawo haka a zukatansu ba yayin ɗaukar hoton, amma tsayuwar da suka yi ta fassara manyan ƙabilun nan uku da Nijeriya ke da su, wato WAZOBIA, ma’ana Yoruba, Hausa da Kuma Igbo.

Idan aka kalli hoton daga hagu, Adesina shi ne na farko inda ya wakilci Yarabawa (WA), sai Shugaba Buhari mai wakiltar ƙabilar Hausa/Fulani (ZO), sannan Ngozi mai wakiltar ƙabilar Igbo (BIA). Lallai Nijeriya ƙasa mai albarka.

Ga ƙarin hotunan Shugaba Buhari daga wajen taron Farisa:

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *