An bai wa kasuwar fanteka ta Kaduna wa’adin mako guda ta tashi

Daga FATUHU MUSTAPHA

Hukumar Raya Birane ta Jihar Kaduna, ta bai wa ‘yan kasuwar sabuwar Kasuwar Fanteka wa’adin mako guda a kan su tattara yanasu-yanasu su bar kasuwar.

Cikin wata sanarwar mai ɗauke da kwanan wata 22, Afrilu, 2021wadda ta sami sa hannun Babban Daraktan Hukumar, Isma’ila Ummaru Dikko, hukumar ta ce wannan umarni ya soma aiki ne daga ranar da aka bada shi.

Hukumar ta ce ta ɗauki wannan mataki ne daidai da Shirin Sabunta Biranen Jihar na Gwamnatin Jihar.

Da wannan gwamnatin jihar ta ce ta bai wa ‘yan kasuwar wa’adin kawana bakwai a kan kowa ya kwashe kayansa daga kasuwar da ke babbar hanyar Nnamdi Azikiwe a jihar.

Tana mai cewa saɓa wannan umarni hukuma ba ta da wani zaɓi face ƙwace kayayyaki tare da rusa shagunan waɗanda suka yi kunnen ƙashi bayan ƙarewar wa’adin da aka shata.