Mahaifiyar Sarkin Kano, Hajiya Maryam ta rasu

Daga UMAR M. GOMBE

Allah Ya yi wa mahaifiyar Sarkin Kano, Hajiya Maryam Ado Bayero rasuwa.

Bayanai daga masarautar Kano sun nuna marigayiyar ta rasu ne a wannan Lahadi a wata asibitin birnin Alƙahira a Kasar Misra, bayan fama da ta yi da rashin lafiya.

Hajiya Maryam ta rasu tana da shekara 86 a duniya. Kuma ita ce mahaifiyar Sarkin Kano, Alhaji Aminu Ado Bayero da Sarkin Bichi, Alhaji Nasiru Ado Bayero.

Ya zuwa haɗa wannan labari, Masarautar Kano ba ta kai ga bada sanarwar lokacin da za a gudanar da jana’izar marigayiyar ba.

Manhaja ta kalato cewa marigayiyar tsohuwar matar marigayi Sarkin Kano ne kuma gimbiya a masarautar Ilorin a jihar Kwara.