Mutum 2 sun mutu a harin da aka kai gidan Gwamna Uzodinma a Imo

Daga WAKILINMU

Sahihan bayanai daga jihar Imo sun tabbatar da wasu mutum biyu sun rasa rayukansu yayin harin da ‘yan bindiga suka kai wa gidan Gwamna Uzodinma da ke Omuma a yankin karamar hukumar Oru ta Yamma a jihar.

Wannan na zuwa ne kwana ɗaya bayan da gwamnan ya sanar da manema labarai cewa an yi nasarar kama wasu mutum 50 da ake zargi suna da hannu a hare-haren da aka kai a Imo lokacin bikin Easter da ya gabata, tare da cewa wasu ‘yan siyasa ne suka ɗauki nauyinsu.

Sai dai Manhaja ba ta samu tabbacin faruwar hakan ba daga wajen Jami’in Haulɗa da Jama’a na ‘Yan Sandan jihar, Mr Orlando Ikokwu, saboda duk ƙokarin da wakilinmu ya yi don jin ta bakinsa nasa kan batun, ya ci tura.

Wani ganau da harin ya faru a gabansa ya faɗa wa Manhaja cewa mutum biyu sun mutu sakamakon harin.

Ya zuwa haɗa wannan labari, babu wani cikakken bayani kan dalilin kai harin, amma ana zargin harin ba ya rasa nasaba da shugaban tsegerun IPOB, Mazi Nnamdi Kanu.

Musamman ma idan aka yi la’akari da barazanar da ya yi kwanaki biyu da suka wuce inda ya ce dole Gwamna Uzodinma da AIG na Zone 9, Ene Okon su wuce in ba haka ba zaɓen gwamna ba zai gudana ba a Anambra. Saboda a cewarsa, su biyun sun zame wa gwagwarmayar Biafra ƙashin maƙogwaro.