Za a soma aikin gyaran gada a Legas

Daga FATUHU MUSTAPHA

Gwamnatin Tarayya ta bada tabbacin cewa nan bada daɗewa ba, za ta soma aikin gyran gadar hanyar zuwa filin jirgin sama a birnin Legas wadda ta ƙone a lokutan baya.

Babban Sakataren Ma’aikatar Ayyuka a Gidaje ta Tarayya, Alhaji Babangida Hussaini, shi ne ya faɗi haka yayin wani rangadi da ya yi a Legas domin duba wasu ayyukan gidaje da hanyoyi da ke gudana a jihar.

Gadar da lamarin ya shafa ta ci wata ne sakamakon haɗarin tankar mai da ya auku a Janairun da ya gabata, kuma a wancan lokaci aka rufe gadar aka hana abubuwan hawa bi ta kanta lamarin da ya haifar da fuskantar matsi wajen zirga-zirga a yankin.

A cewar Sakataren kafin ƙarshen watan Maris za a soma aikin gyaran gadar, tare da cewa tuni an soma shirye shiryen haka.

Kazalika, ya ce sun lura gine-ginen da aka yi su ba a bisa ƙa’ida ba a gefen hanyar zuwa filin jirgin saman waɗanda aka ciccire a baya, an sake maido da su, don haka ya ce za a sake komawa a ciccire su.