Daga UMAR M. GOMBE
Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya yi martani kan harin da ‘yan bindiga suka kai wa Gwamna Samuel Ortom na jihar Binuwai.
‘Yan bindiga sun bude wa tawagar gwamnan wuta ne a lokacin da yake dawowa daga gonarsa a ranar Asabar da ta gabata.
Tun bayan aukuwar lamarin ‘yaan ƙasa da dama sun yi ta faɗin albarkacin bakunansu game da harin inda wasunsu suka yi kira ga gwamnatin tarayya da ta magance ƙallubalen tsaro da ke adabar sassan ƙasar nan.
cikin sanarwar da ya fitar a daren Lahadi, shugaba Buhari ta bakin kakakinsa Garba Shehu, ya yi tir da harin inda ya buƙaci hukumomin tsaro su da gudanar da cikakken bincike.
Haka nan, Ƙungiyar Gwamnonin Arewa ta yi Allah-wadai da harin da ‘yan bindiga suka kai wa Gwamna Samuel Ortom, tare da bayyana lamarin a matsayin abin damuwa.
Shugaban ƙungiyar kuma gwamnan Jihar Filato, Simon Lalong ne ya bayyana haka a wata sanarwa da ya fitar ta hannun Daraktansa na Yaɗa Labarai da hulɗa da jama’a, Dr. Makut Macham, a garin Jos.
Gwamnan ya ce ya zama wajibi a binciki lamarin, tare da bayyana harin a matsayin wani mataki na neman haddasa rashin lumana a Jihar Binuwai da ma ƙasa baki ɗaya.
Haka nan ya ƙalubalanci hukumomin tsaro kan su gudanar da bincike mai zurfi domin gano waɗanda ke da hannu a harin da ma waɗanda suka ɗauki nauyin kai harin.
Daga nan, ya yaba da ƙoƙarin jami’an tasron da suka yi ƙoƙarin daƙile hari inda suka ceci Gwamna Ortom da ayarinsa.
Asabar da ta gabata ‘yan bindigar suka kai wa Ortom da ayarinsa hari a ƙauyen a Tyo-Mu da ke kusa da Makurdi babban birnin jihar.