Nagarta ke sa a bai wa mutum sarauta – Sarkin Zabarmawan Kabi

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Sarkin Zabarmawan Kabi Honarabul Sama’ila Abdulmumini Kamba (Ganda) tsohon kakakin majalisar dokoki ta jihar Kebbi ya bayyana cewa nagarta ce sanya a bai wa mutum sarauta.
Ya yi wannan bayanin ne jim kaɗan bayan kammala naɗin sa a matsayin Kakakin Gwandu a fadar Sarkin Gwandu ƙarshen makon nan lokacin da ya ke zantawa da manema labarai.

Alhaji Sama’ila Ganda ya ce na farko dai ya yi aiki da mai martaba Sarkin Kabin Argungu a baya wanda kuma basaraken ya ga irin ƙoƙarin da ya ke yi a wajen aiki da kuma fafutukar da ya ke yi wajen haɗin kan Zabarmawa daga dukkan masarautun jihar Kebbi da kuma ƙetare.
Haka-zalika a lokacin da ya ke kakakin majalisar dokoki ta jihar Kebbi mai martaba Sarkin Gwandu ya ga irin gudummawar da ya ke bayarwa saboda haka shi ma ya yanke shawarar ba shi sarautar Kakakin Gwandu sai dai da ya ke lokacin ana fama da matsalar Korona sai yanzu aka yi naɗin sarautar duk da ya ke ya bar majalisar.

Ya ce yana da kyau duk inda mutum ya sami kan sa ya zamo mutum mai dattako wanda shi ne ke sanya masarautu ke janyo shi kusa da su don ƙarin samun haɗin kan al’umma musamman yan siyasa.

Sau da yawa za ka ga idan mutum ya bar ofis na siyasa a manta da shi amma duk wanda ke da dattijantaka da riƙon amana ko bayan ya bar ofis na siyasa ba za a manta da shi ba.

By ukarofi

Leave a Reply