Legas: Hukumar Kwastam ta kama taramo katan 554

Daga AISHA ASAS

Ofishin Hukumar Yaƙi da Fasa-ƙwauri ta Nijeriya (NCS) da ke Apapa a Legas, ya ce ya kama wani kwantena mai lamba 1793504 wanda aka yi amannar tais (tiles) ne aka ɗauko, amma bayan da aka zurfafa bincike sai aka gano katan-katan na ƙwayar taramo guda 554 maƙare a cikin sunduƙin.

Da yake yi wa manema labarai bayani a ranar Alhamis da ta gabata Shugaban Hukumar na Apapa, Controller Malanta Yusuf, ya ce kimanin makonni uku da kama aiki a Apapa, sun yi nasarar kama sunduƙai da dama ɗauke da kayayyakin da aka haramta shigo da su cikin ƙasa.

Haka ma sun kama wasu kayayyakin da doka ta yarda a shigo da su amma aka shigo da su ba tare da cika ƙa’idojin da aka shimfiɗa ba.

Ya ce, sun cim ma nasrar kama kayayyakin ne sakamakon bayanan sirri da suka tattara da kuma tsananta binciken jami’ansu.

Ya ƙara da cewa, za su ci gaba da zurfafa bincike har sai sun gano waɗanda ke da hannu wajen shigo da waɗannan kayyaki don su fuskanci hukunci.

Ya ce, kamata ya yi mutane su zamo masu aikata abin da ya dace ko da kuwa babu mai ganin su.