‘Yan sanda sun ceci motocin BRT a Legas

Daga WAKILINMU

Rundunar ‘yan sanda a Legas, ta ce ta yi nasarar daƙile harkokin ɓatagarin da suka yi yinƙurin yi wa fasinjoji fashi a dogayen motocin safa na BRT a lokacin da aka samu tsaikon abubuwan hawa sakamakon wani haɗari da ya auku.

A cewar sanarwar da ta fito ta hannun jami’in hulɗa da jama’a na ‘yan sandan jihar, CSP Olumuyiwa Adejobi, ganin abin da ke faruwa sai kwamishinan ‘yan sandan jihar, CP Hakeem Odumosu ya bai wa jami’an sashen kai ɗaukin gaggawa (RRS) na rundunar umarnin su je su tabbatar da lumana a yankin da lamarin ya shafa.

Daga bisani, jami’an sun isa yankin kan lokaci tare da yin abin da ya kamata inda suka bai wa dogayen motocin safan kariya tare da yi musu rakiya domin kare su daga sharrin ɓatagarin.

Tuni kwamishinan ‘yan sandan ya bada umarnin a kamo ɓatagarin da suka takura wa jama’a a wurin da hadarin ya auku a Larabar da ta gabata don su fuskanci hukunci daidai da laifin da suka aikata.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *