WTO: Ba domin Buhari ba da ban kaiblabari ba – Dr Ngozi

Daga FATUHU MUSTAPHA

Shugabar Hukumar Cinikayya ta Duniya, Dr. Ngozi Okonjo-Iwela, ta ce taimako da goyon bayan da shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya yi mata sun yi matuƙar tasiri wajen ba ta nasarar ɗarewa kujerar jagorancin hukumar WTO.

Ngozi ta bayyana haka ne a lokacin da ta kai wa Buhari ziyara don nuna godiyarta, tana mai cewa zaɓin da Buhari ya yi mata wajen tsayawa takara da ɗaruruwan wasiƙun da ya rubuta wa shugabannin duniya da kiran da ya yi musu ta waya domin goya mata baya sun taimaka mata wajen samun nasara.

Ta ci gaba da cewa da ba dan goyan bayan da shugaba Buhari ya ba ta ba, da zai yi wuya ta ɗare kujerar da take kai a yau.

A nasa ɓangaren, shugaba Buhari ya ce duk da goyan bayan da gwamnatinsa ta bayar, Ngozi Okonjo-Iweala na da ƙwarewar da ake buƙata na jagorancin WTO.

Buhari ya taya Okonjo-Iwela murna tare da yi mata fatan alheri wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyanta.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *