03
Dec
Daga AMINA YUSUF ALI Gwamnatin Nijeriya ta bayyana wasu dalilai da suka hana ta taɓuka komai a game da hauhawar farashin gas a ƙasar nan. Gwamnatin ta bayyana cewa, abin ya fi ƙarfinta ne. Saboda ita iskar gas, gwamnati ba ta ɗauke mata tallafi ba, sannan kuma farashinta ikon kasuwannin ƙasashe ne ba ƙasa guda ba. Ministan albarkatun man fetur, Mista Timipre Sylva, shi ya bayyana haka a ranar Talatar da ta wuce a yayin da yake mayar da martani a game da tambayar da aka yi masa game da dalilin da ya kawo tashin gwauron zabi na farashin gas…
