Majalisar Dattawa za ta samar da hukumar kula da gidaje da filaye

Daga AMINA YUSUF ALI

A yanzu haka dai majalisar dattawan Nijeriya tana gab da tabbatar da ƙudirin samar da hukumar da za ta dinga tafiyarwa da kuma kula da hada-hadar gidaje da filaye. A ƙoƙarinta na ceto dubban ‘yan Nijeriya da suke faɗawa komar mazambata a koyaushe.

An shigar da wannan ƙuduri ne domin kawo saiti a harkar hada-hadar gidaje da filayen wacce sam ba saiti a cikinta. Wacce hakan ya sa wasu ɓata-garin ke amfani da damar don turmusa hancin wasu ‘yan Nijeriya.

Shi dai wannan ƙuduri wanda Sanata Aliyu Wamakko (APC, Sokoto) ya ɗauki nauyi a yanzu haka ya shige karatu na uku a majalisa.

Ƙudirin an kawo shi kuma an karanta shi a zauren majalisar ne tun ranar 28 ga watan Afrilun 2021 ne, kuma a 22 ga watan Yunin 2021 ya shige karatu na biyu a zauren majalisar.

A ranar Larabar da ta wuce ne aka zauna don tattaunawa a game da shi kuma har ma ya wuce karatun na uku.

A cewar majalisar, samar da hukumar zai daƙile matsalolin gidajen da wasu dillalan suke ha’intar mutane su karɓe musu kuɗaɗe ba tare da ba su gidaje ba. Sannan da cinikin gidaje ba bisa tsari ba. Wanda a cewar su abin ya zama ruwan dare a garuruwan Legas da Abuja.