Ɗan jarida ya bayyana yadda za a kasafta kuɗin Davido ga gidajen marayu

Daga AMINA YUSUF ALI

Fitaccen ɗan Jaridar nan a Kano, Ibrahim Ishaq Ɗanuwa Rano ya bayar da shawarar yadda ya kamata a raba kuɗin mawaƙi Davido Naira miliyan 250 da ya ce ya bayar da su kyauta domin tallafa wa gidajen marayu a Nijeriya.

Ibrahim Ɗanuwa Rano, wanda shi ne ke gabatar da shirin siyasa na ‘Kowanne Gauta’ a gidan rediyon ‘freedom da ke jihar Kano ya bayyana hakan ne ranar Asabar ɗin da ta wuce a shafinsa na fesbuk kamar haka, “Aƙalla idan aka ɗauki gidajen Marayu goma a kowacce jiha da ke faɗin Najeriya, za su iya amfana da kayan abinci ko zallar kuɗi da ya tasam ma kusan Naira dubu ɗari bakwai, daga cikin Naira Miliyan ɗari biyu da hamsin da fitaccen mawaƙi Davido zai miƙa ga masu rangwamen gata“.

Ya ƙara da cewa “Idan ba mu manta ba, Mawaƙi Davido ya tara kuɗaɗen ne ta hanyar neman gudunmowa daga ‘yanuwa da abokanan arziki domin taya shi murnar ƙarin shekara. kuma ban tara masa kimanin Miliyan 200 shi ma ya ƙara miliya50 daga aljihunsa, tare da kafa kwamitin nagartattun mutane da za su yi aikin raba kuɗaɗen ga gidajen marayu a dukka jihohin Najeriya.”

Haka kuma ɗan jaridar ya yi addu’ar Allah ya sa masu hali su yi koyi da wannan halin karamci da mawaƙin ya yi. Tare da yin fatan Allah ya sa mawaƙin mai ruhin taimako da tausayi ya amshi Musulunci.