Kamfanonin Nijeriya uku sun ciyo Dala $480,000 a gasar Jack Ma

Daga AMINA YUSUF ALI

Kamfanonin Nijeriya guda uku sun samu nasarar lashe gasar Jack Ma ta ‘Zakarum kasuwancin Afirka’ sun samu kyautar Dalar Amurka $480,000.

Shi dai wannan shiri wanda biloniyan nan ɗan asalin ƙasar Chana, Jack Ma ya ɗauki nauyin sa ya raba dubunnan ɗaruruwan daloli domin tallafa wa ƙananan kamfanoni a yunƙurinsa na ganin ya tallafa wa ƙasashen Afirka don warware musu matsalolinsu.

Kamfanonin guda uku sun yi awon gaba da kusan Dalar Amurka rabin miliyan. Wato gwari-gwari, akwai wani kamfanin sarrafa kayan abinci a Legas mai suna, Releaf wanda ya zo ta biyu a gasar ya samu dala dubu ɗari biyu da hamsin $250,000.

Sai kuma sauran kamfanonin guda biyu, Gricd da Publiseer waɗanda suka zo a cikin jerin kamfanoni goma na farko a nasarar zaɓen su kuma sun samu dala dubu ɗari-ɗari kowannensu $100,000.

Bayan waɗannan kyaututtukan kuma, ana sa ran kowanne zakara zai samu ƙarin tagomashin Dala dubu goma-goma, don halartar taron horaswa na ‘yan Kasuwa wanda kamfanin Alibaba dake Hangzhou, a ƙasar Chana zai ɗauki nauyin shiryawa.

Shi dai wannan taron ba da kyaututtuka na zakarun kasuwanci na Afirka, an shirya shi ne ranar Larabar da ta wuce, a ƙasar Chana. Wanda biloniyan ƙasar mai suna Jack ma ya ɗauki nauyin taron da kyaututtukan.