Ko layin wayar Starlink zai iya gogawa da MTN, Airtel da Glo?

Daga AMINA YUSUF ALI

Ko shin sabon layin sadarwa na Starlink zai iya goga kafaɗa da kamfanonin sadarwa na MTN da Glo a Nijeriya? Wannan ita ce tambayar da akasarin masu bibiyar al’amuran yau da kullum suke yi kenan. 

Shi dai wannan sabon layin waya mai suna Starlink mallakin kamfanin wannan biloniyan ba’amurken ne, Elon Musk wanda alƙaluma suka tabbatar da cewa ya fi kowa ƙarfin arziki a Duniya.

A yanzu haka rahotanni sun tabbatar da cewa Elon Musk yana da ƙudurin kamfanin zai shigo ƙasar Nijeriya da ƙarfinsa ya kafa sansanin kasuwanci a Nijeriya a shekara mai zuwa domin yin gogayya da sauran kamfanonin sadarwar da suke a ƙasar kamar yadda wani bayani daga kamfanin ya bayyana. 

Rahotanni daga jaridar ‘Ripples Nigeria’ sun bayyana cewa, tuni wakilai daga kamfanin sadarwar na starlink wanda shi ne zai wakilci SpaceX,  sun shigo ƙasar Nijeriya a watan Mayu, 2021 sun kawo ziyara har ma suka samu tattaunawa da Hukumar Sadarwa ta Ƙasa wato NCC.

Tattaunawar tasu ta kasance a kan yadda tsarin shigo da sabon layin sadarwar na Starlink a kasuwar sadarwar ƙasar da kuma neman lasisi ga kamfanin na Biloniya Musk wanda ya sha alwashin samar da tsarin sadarwa da zai mamaye kaso biyar na ƙasashen Duniya har ma da Nijeriya. Wanda kamfanin ya sanya ranar fara aikinsa a Nijeriya ba gudu ba ja da baya a cikin 2022. Abinda majiyarmu ta bayyana cewa ya lamushe Dalar Amurka biliyan biyar zuwa goma ana kuma sa ran ma nan gaba ya kai Dala biliyan ashirin zuwa talatin. 

Shi dai Elon Musk shi ne mutumin da ake sa ran saura ƙiris ya zama Triliyoniya na farko a Duniya. Wato mamallakin Dala  biyan dubu a Duniya.