Abinda ya sa ba za mu iya sauke farashin gas ba – Gwamnati

Daga AMINA YUSUF ALI

Gwamnatin Nijeriya ta bayyana wasu dalilai da suka hana ta taɓuka komai a game da hauhawar farashin gas a ƙasar nan. Gwamnatin ta bayyana cewa, abin ya fi ƙarfinta ne. Saboda ita iskar gas, gwamnati ba ta ɗauke mata tallafi ba, sannan kuma farashinta ikon kasuwannin ƙasashe ne ba ƙasa guda ba.

Ministan albarkatun man fetur, Mista Timipre Sylva, shi ya bayyana haka a ranar Talatar da ta wuce a yayin da yake mayar da martani a game da tambayar da aka yi masa game da dalilin da ya kawo tashin gwauron zabi na farashin gas ɗin girki abinda ya tilasta wasu ‘yan ƙasa amfani da wasu makamashin saɓanin gas ɗin. Inda ya ce, “Gwamnatin Tarayya ba za ta iya komai ba don shawo kan matsalar tashin farashin na gas ɗin ba”.

A yayin zantawar tasa  da ‘yan jaridu a fadar shugaban ƙasar Nijeriya dake Abuja, Mista Sylva ya ƙara da cewa, shi gas ɗin girki abu ne da ba wanda zai iya yanke masa takamaiman farashi.

 idan za a iya tunawa, farashin na gas kwana-kwanan nan ya yi matuƙar tashi a Nijeriya. Inda har ya ninka fiye da kuɗin da ake sayar da shi a bara. Abinda ya jawo wasu magidantan suka fara komawa amfani da icce ko gawayi domin an cire tallafin kan gas ɗin. Sannan kuma harajin VAT na shigo da gas ]in daga ƙasashen waje shi ma ya taimaka wajen hauhawar farashinsa. Don haka a cewar sa, Gwamnati ba ta da iko a kan hawa ko saukar farashin gas ɗin. Abu ne da ya shafi dukka ƙasashen Duniya.

Ministan ya ƙara cewa, a yanzu haka a ƙasar Turai ma an samu irin wannan makamanciyar hauhawar farashin na gas abinda ya jawo aka yi zanga-zangar rashin amincewa. To yanzu zancen da ake yi, farashin gas ɗin nahiyar Turai shi ya jawo hauhawar farashin gas a faɗin Duniya. Wannan da ma kuma ƙarin harajin VAT a kan gas dukka sun taimaka wajen ƙaranci da tsadar gas ɗin. 

Hakazalika, yawan shigo da gas ɗin daga ƙasar waje shi ne ya kashe kasuwancin samar da gas na cikin gida, a Nijeriya. 

A cewar Mista Sylva, waɗannan dalilai su suka sa gwamnati ta kasa saita farashin gas ɗin yadda za ta sakko da shi. Amma a cewar sa, yanzu haka gwamnatin Buhari tana iya ƙoƙarinta wajen ganin ta kawo ƙarshen tashin farashin nasa. Domin sauƙaƙa wa ‘yan Nijeriya tsadar rayuwa.