Hakimin da ya shekara 68 yana mulki ya rasu a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Allah ya yi wa Sarkin Ban Kano Alh. Dr. Mukhtar Adnan rasuwa a daren jiya juma’a,

Marigayin ya rasu yana da shekara 95 a duniya,

Babban ɗansa Baba Ado ya shaida wa manema labarai cewa mahaifin nasa ya rasu ne dab da asubahin ranar Juma’a a sibitin UMC Zahir da ke unguwar Jan Bulo inda ya yi jinya.

An yi jana’izarsa bayan Sallar Juma’a a babban masallacin garin Ɗanbatta, da ke jihar Kano.

Marigayi Alhaji Mukhtar Adnan yana daga cikin masu zaɓen Sarkin Kano, wanda kuma shi kaɗai ne ya kafa tarihi, inda ya zaɓi sarakunan Kano guda huɗu da suka haɗa da Sarkin Kano Alhaji Muhammadu Inuwa da Alhaji Ado Bayero a 1963, da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II a 2014 da kuma Sarkin Kano Alhaji Aminu Ado Bayero a 2020.

Shi ne ya fi kowa daɗewa a matsayin hakimi a masarautar Kano, inda ya shafe shekara 68 a matsayin Hakimin ƙaramar hukumar Ɗanbatta,

Tun a zamanin Sarkin Kano Muhammadu Sanusi ne dai ya naɗa shi a matsayin Sarkin Ban Kano kuma Hakimin Ɗanbatta a shekarar 1954.

Marigayin ya rasu ya bar ‘ya’ya da dama cikinsu har da Dakta Mansur Mukhtar, tsohon Ministan Kuɗi na Najeriya, wanda kuma a yanzu mataimakin shugaba ne a Bankin Musulunci na Duniya da ke da cibiya a ƙasar Saudiyya.