Tsadar abinci: Gwamnatin Nijar za ta fara sayar wa da talakawa kayan abinci da kanta

Daga AMINA YUSUF ALI

A yayin da ‘yan ƙasar Nijeriya suke kokawa da matsananciyar tsadar abinci wanda ya jefa su a ƙangin rayuwa, ita kuma ƙasar Nijar ta karɓe ragamar sayar da abinci daga hannun magadan gari domin fara sayar da shi a farashi mai rahusa ga talakawan ƙasar, wadanda ke shan wahala wajen samun wadataccen abincin. Tuni wannan matakin ya haddasa cece-kuce a faɗin ƙasar, inda wasu ke lale marhabin da tsarin, wasu kuma suke adawa.

Gwamnatin Nijar ta karɓe ragamar sayar da abinci daga hannun magadan gari domin fara sayar da shi a farashi mai rahusa ga talakawan ƙasar, waɗanda ke shan wahala wajen samun wadataccen abincin.

Tuni wannan matakin ya haddasa cece-kuce a faɗin ƙasar. Yayin wasu ke lale marhabin, wasu kuma ke adawa.

Jaridar yanar gizo ta Legit ta bayyana cewa, duba da yadda talakawa ke shan wahala, gwamnatin jamhuriyar Nijar ta yanke shawarar fara sayar da abinci da kanta.

A rahoton da muka samu, gwamnati ta ce ta karɓe ragamar sayar da kayan abinci da wasu ɗaiɗaiku ke da shi a ƙasar. A wani saƙon sautin da Legit.ng Hausa ta samo daga RFI, ta ce ministan cikin gida na jamhuriyar ta Nijar ne ya karɓe ragamar sayar da abinci daga magadan gari domin rage wa talakawa raɗaɗi.

Tuni an tura wasiƙu ga waɗanda ke da hannu a harkokin sayar da abinci a ƙasar domin sanar da su wannan cigaba, wanda ya fara daga jihar Damagaram.

Abdu Sallau Kogo muƙaddashin magatarka na ofishin gwamnan jihar Damagaram ya shaida wa majiyarmu cewa: yanzu haka an daina sayen abinci a hannun ‘yan kasuwa sai gwamnati. Wannan ya jawo ce-ce-ku-ce a nan ƙasar Nijeriya inda al’umma suke ganin gwamnati ta ƙyale ‘yan kasuwa suna cin karensu ba babbaka.