‘Yan sandan Zamfara sun kama wata mata bisa zargin ba wa ‘yan bindiga harsashi

Daga SANUSI MUHAMMAD a Gusau

Rundunar ‘yan sandan jihar Zamfara sashen Tactical Operatives tare da haɗin gwiwar FIB/STS ƙarƙashin jagorancin DSP Hussaini Gimba, sun kama wata mata mai suna Fatima Lawali ‘yar shekara 30 da ta amsa laifin yin safarar harsasai ga ‘yan bindiga a Gusau babban birnin jihar Zamfara.

Kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ayuba N. Elkana ne ya bayyana hakan a wani taron manema labarai a ranar Juma’a.

A cewarsa, an kama wanda ake zargin ne a unguwar Gada Biyu da ke ƙarƙashin ƙaramar hukumar Bunguɗu a Gusau babban birnin jihar Zamfara.

Ya ce, “A ranar 25 ga Oktoba, 2021 da misalin ƙarfe 0930 na safe, rundunar ‘yan sanda tare da haɗin gwiwar FIB/STS ƙarƙashin jagorancin DSP Hussaini Gimba sun samu nasarar cafke Fatima Lawali wadda ake zargi da safarar alburusai ga ‘yan bindiga a jihar.”

Ya bayyana cewa an samu nasarar bankaɗo harsashi har guda 991 na Ak-47 daga hannunta da ta shirya kai wa wani ƙasurgumin ɗan bindiga mai suna Ado Alero da ya addabi jihar Zamfara da sauran jihohin da ke maƙwabtaka da ita.

A zantawa da manema labarai, wadda ake zargin A’isha Lawali ta amsa laifin ta, inda ta ce an biya ta kuɗi N50,000 a karon farko da kuma Naira 30,000 a karo na biyu wajen safarar harsasan ga ‘yan ta’adda kafin ‘yan sanda su kama ta a Gusau.

Ta ƙara da cewa wani Sama’ila ne ya aike ta ga manyan kwamandojin ‘yan bindiga daga Zamfara zuwa ƙaramar hukumar Gada a jihar Sakkwato da harsashi guda 991 kafin ‘yan sanda su kama ta a Gusau.

CP Ayuba ya bayyana cewa, ana ci gaba da gudanar da bincike kan lamarin domin ci gaba da shari’a kan wanda ake zargin.

Kwamishinan ya ƙara da cewa rundunar ta kama wani mai suna Bello Mu’azu mai shekaru 29 a duniya bisa zargin yunƙurin yi wa yarinya ‘yar shekara 4 fyaɗe mai suna Aisha Buhari a garin Talata Mafara hedikwatar ƙaramar hukumar Talata Mafara ta jihar Zamfara.

“A ranar 24 ga Nuwamba, 2021 misalin ƙarfe 1500 na safe, rundunar ‘yan sanda ta ƙaramar hukumar T/Mafara ta samu ƙorafi kan wanda ake zargin Bello Mu’azu, cewa a daidai ƙarfe biyu na ranar, wani ya ga wanda ake zargin tare da wanda ake yunƙurin yi wa fyaɗen a cikin wani lungu yana ƙoƙarin cire mata wando don yi mata fyade”. CP Ayuba ya ce.

A cewar kwamishinan ana cigaba da gudanar da bincike kan lamarin domin a kai shi kotu.