Sabon harin Filato ya laƙume rayuka 10 da gidaje 30

Daga BASHIR ISAH

Rahotanni daga yankin ƙaramar hukumar Bassa a jihar Filato, sun nuna cewa aƙalla mutane 10 sun mutu sannan an ƙona gidaje sama 30 sakamakon wani sabon hari da aka kai da sanyin safiyar Juma’a a ƙauyen Te’egbe da ke yankin.

Mai magana da yawun ‘yan sandan jihar, Ubah Ogaba, ya tabbatar da aukuwar harin cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Juma’a, inda ya ce wasu da ba a kai ga sanin ko su wane ne ba sun kai hari a ƙauyen Te’egbe da ke yankin ƙaramar hukumar Bassa a jihar.

Ya ce mutum 10 sun mutu sakamakon harin, yayin da aka ƙona gidaje kimanin guda 30.

Mr Ogaba ya ce kwamishinan ‘yan sandan jihar ya bada umarnin gudanar da bincike kan lamari domin gano waɗanda suke da hannun a cikinsa tare da hukunta su yadda ya kamata.