Da ɗumi-ɗumi: Aisha Musa Dalil ta zama gwarzuwar gasar ‘Hikayata’

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

Aisha Musa Dalil, ita ce ta zo ta farko a gasar Hikayata ta BBC Hausa ta shekarar 2021, haifaffiyar Jihar Kaduna, wanda ta yi karatun firamare da sakandare duk a jihar Kaduna, sannan yanzu haka tana karatu a Jami’ar Umaru Musa YarAdua da ke Katsina, inda take karantar harsunan Ingilishi da Faransanci a fannin kimiyyar harshe.

Aisha Musa Dalil ta shiga gasar Hikayata ta BBC Hausa da labarinta mai taken ‘Haƙƙina’, wanda jigonsa ya karkata kacokan akan fyaɗe kamar yadda ta bayyana a tattaunawar da ta yi da jaridar Manhaja kafin bayar da kyaututtuka, ranar Juma’a a Abuja.

“Na ɗauki jigon fyaɗe ne ganin yadda ya zama ruwan dare a wannan zamani, babu tausayi ko tsoron Allah za ka samu wani azzalumi ya kama ƙaramar yarinya ya lalata mata rayuwa,” inji Aisha Musa Dalil.

Haka zalika, gwarzuwar gasar ta bayyana cewa ba ta taɓa buga littafi domin fitar da shi ga makaranta da ‘yan kasuwa ba, ta ce ita marubuciyar yanar gizo ce, ta kuma rubuta littafai irin su: ‘So Ne Silar Hawayena’ da ‘So ne Ko Qiyayya?, ‘Amanar Mu’ da kuma wani na turanci ‘Life of Hidaya.

Aisha Musa Dalil ta kuma ce yawan karance-karance littafan Hausa su ne suka fizgeta ga sha’awar taunduma harkar rubutu, inda ta ce littafan Fauziyya D. Suleiman da Jamila Umar Tanko sun taka muhimmiyar rawa wajen zamewarta marubuciya.

Da aka tambayi Aisha Musa ko yaya ta ji a lokacin da BBC ta fitar da sunayen gwaraza uku da suka lashe gasar ta bana, sai ta ce ta yi farin cikin mara misaltuwa.

“Ai in faxa maka da na ga sunana a ciki sai da na wuntsulo daga kan gado saboda tsabar daɗi da farin ciki.

Aisha Musa

“Sannan na faɗi a ƙasa na yi wa Allah sujuda da kuma addu’o’i. To gaskiya ba ƙaramin farin ciki na yi ba,” inji ta.

Aisha ta kuma bayyana cewa tun tana firamare take ƙirƙirar tatsuniya da kanta, wadda ba ji ta yi daga bakin wani ba ko daga iyaye da kakanni kamar yadda yake a al’ada.

Aisha Musa Dalil ta samu kyautar dala 2,000 da kuma kambun karramawa. Tana da shekara 18 a duniya.