Kasuwanci

Gobarar gas ta janyo asarar rayuka biyar da dukiyoyi a Abuja

Gobarar gas ta janyo asarar rayuka biyar da dukiyoyi a Abuja

Daga AMINA YUSUF ALI Aƙalla mutane biyar ne har da yara guda uku suka samu munanan raunuka da kuma shaguna da suka ƙone a sakamakon fashewar silindar gas wacce ta fashe ta tasar da gobara a unguwar Gwagwalada da ke Birnin Tarayyar Abuja.   Al'amarin ya faru ne a wani kango kusa da unguwar Dagiri wacce ke kusa da titin Abuja/Lokoja da ke unguwar Gwagwalada a Abuja.   Shaidun gani da ido sun bayyana wa majiyarmu cewa, a take aka garzaya da majikkatan i zuwa asibitin Zamad da yake a yankin Dagari a Gwagwalada. Hakazalika, shaidun sun bayyana cewa, musabbabin gobarar shi…
Read More
Attajiri Otedola ya saka First Bank a aljihunsa

Attajiri Otedola ya saka First Bank a aljihunsa

Daga AMINA YUSUF ALI Yanzu haka, biloniyan ɗan kasuwar nan mai suna Femi Otedola shi ne mutum na farko daga cikin jerin masu hannun jari a bankin First Bank. Biloniyan ya samu nasarar ɗarewa kan matsayin wanda ya fi kowa zuba hannun jari a bankin bayan ya sake sayen ƙarin kaso 2.5 na hannun jarin kamfanin FBNH wanda FBNH shi ne ubangidan bankin na First Bank. Rahotanni sun bayyana cewa, a halin yanzu ma Otedola yana da hannun jari kaso 7.57 a FBNH. Abinda ya kai har ya doke Tunde Hassan-Odukale, Ciyaman ɗin FBNH a ƙarfin hannun jari a kamfanin.…
Read More
Ku kasance cikin shirin ƙarin haraji – Ministar Kuɗi ta gargaɗi ‘yan Nijeriya

Ku kasance cikin shirin ƙarin haraji – Ministar Kuɗi ta gargaɗi ‘yan Nijeriya

Daga AMINA YUSUF ALI Ministar Kuɗi, kasafi da tsare-tsare ta Nijeriya, Hajiya Zainab Ahmad ta gargaɗi 'yan ƙasar a kan su kasance cikin shirin samun ƙarin haraji. A cewarta, ba makawa za a samu ƙarin haraji a kan wasu mutane da wasu sana'o'i a wannan matsakaicin zangon.  Ministar ta bayyana haka ne ga 'yan kasuwa yayin gudanar da taron jin ra'ayoyin jama'a a game da kasafin kuɗi na shekarar 2021 ranar Litinin ɗin da ta gabata a Abuja. Hajiya Zainab ta ƙara da cewa, Gwamnatin tana tunanin ƙarin harajin ne domin neman farfaɗo da tattalin arzikin ƙasar nan. Shi dai…
Read More
Bankin Duniya ga Nijeriya: Ku yanka wa mashaya taba, barasa da kayan zaƙi haraji

Bankin Duniya ga Nijeriya: Ku yanka wa mashaya taba, barasa da kayan zaƙi haraji

Daga AMINA YUSUF ALI Bankin Duniya ya nemi Gwamnatin Nijeriya da ta yanka wa mashaya barasa da taba da sauran kayan sha na zaƙi haraji domin inganta lafiyar al'umma. Daraktan ƙasa na Bankin Duniya a Nijeriya, Shubham Chaudhuri, shi ya bayyana haka a ranar Juma'ar da ta gabata. Inda ya ƙara da cewa, in dai har ana son inganta lafiyar 'yan Nijeriya, dole a sanya musu haraji mai nauyi a kan shan abubuwan da aka san suna cutar da al'umma saboda tsananin illarsu ga lafiyar mutane. Hakan a cewar sa wata hanya ce ta ceto rayuwar dubban 'yan Nijeriya daga…
Read More
‘Yan Nijeriya miliyan 109 ne za su faɗa talauci nan da 2022 – Ministar kuɗi

‘Yan Nijeriya miliyan 109 ne za su faɗa talauci nan da 2022 – Ministar kuɗi

Daga AMINA YUSUF ALI A ranar Talatar da ta gabata ne, gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa, jimillar adadin yawan matalautan Nijeriya zai kai miliyan 109 nan da ƙarshen shekara mai kamawa ta 2022. Jaridar Daily Trust ta rawaito cewa, Ministar kuɗi da tsara kasafin kuɗin ƙasa, Zainab Ahmed ta bayyana cewa, adadin matalauta a Nijeriya zai tasamma miliyan 109 nan da ƙarshen shekarar baɗi. Inda ta ƙara da cewa, za a samu ƙarin wasu 'yan Nijeriya da za su dulmiya a cikin talauci nan da ƙarshen 2022 a sakamakon lara ɓarkewar annobar cutar COVID-19 . Abinda zai kama jimlar yawan…
Read More
Ɗan Majalisa ya ɗauki nauyin horas da mutane 387, kasuwanci a Ƙauru

Ɗan Majalisa ya ɗauki nauyin horas da mutane 387, kasuwanci a Ƙauru

Daga MOH BELLO HABIB a Zariya Wani Ɗan Majalisar wakilai na tarayyar Nijeriya mai wakiltar mazaɓar Ƙauru cikin jihar Kaduna, Honorabul Mukhtar Zakari Isa Chawai ƙarƙashin kulawar Hukumar Sanya Ido a kan kayayyakin dake amfani a Nijeriya (Nigeria Bio safety Management Agency) ya ɗauki nauyin horas da matasa 387 sanin dabarun kasuwanci a mazaɓarsa. Ɗan majalisar ya faɗi wannan batu a yayin rufe taron horas da wasu ƙarin matasan har su 27 na tsawon kwanaki 3 da ya ɗauki nauyin gudanarwa a ɗakin taro dake garin Ƙauru ranar Lahadin da ta gabata. Ya ce, wannan horaswa ita ce karo na…
Read More
Yadda Ɗangote ya wuce ƙasashen Afirka fiye da guda 30 a arziki

Yadda Ɗangote ya wuce ƙasashen Afirka fiye da guda 30 a arziki

Daga AMINA YUSUF ALI A halin yanzu dai arzikin attajirin biloniyan nan ɗan asalin Nijeriya, Aliko Ɗangote ya ƙara haɓaka inda a yanzu haka ma ya zarce fiye da ƙasashen Afirka guda 30 a arziki. Al'amarin ya faru ne bayan attajirin biloniyan wanda kuma shi ne mutumin da ya fi kowa arziki a Afirka ya ci ribar Naira biliyan N968 a cikin watanni goma sha ɗaya kacal. Jaridar Bloomberg ta rawaito cewa, a yanzu haka ƙarfin arzkin Ɗangote ya kai dalar Amurka $20.1 billion wato Naira tiriliyan takwas da biiyan huɗu a kuɗin Nijeriya (N8.4 trillion). Majiyarmu ta ƙara da…
Read More
Yadda wani matashi ya auri ’yan mata 9 a rana ɗaya

Yadda wani matashi ya auri ’yan mata 9 a rana ɗaya

Wani matashi ɗan ƙasar Brazil, Arthur O Urso, ya shiga kundin tarihi na duniya bisa auren mata 9 a rana ɗaya saboda soyayya. Rahotanni sun bayyana cewa, angon kyakkyawa ne sosai abin kwatance, wanda hakan ya sa kusan duka ’yan matan garin suka raja’a masa. Arthur ya bayyana cewa, babban dalilinsa na yin haka shi ne don nuna tsantsar soyayya da kuma nuna adawa da auren mace ɗaya tilo. Ya ƙara da cewa, ya yi haka ne don nuna soyayya da nuna adawa da auren mace ɗaya. An ɗaura auren ne a wani cocin Katolika da ke birnin Sao Paulo…
Read More
’Yan kasuwa a Nijeriya sun ƙalubalanci ECOWAS kan kan rufe iyakar Ghana

’Yan kasuwa a Nijeriya sun ƙalubalanci ECOWAS kan kan rufe iyakar Ghana

Daga AMINA YUSUF ALI A ranar Larabar da ta gabata ne wasu 'yan kasuwa a Nijeriya suka nuna fushinsu a game da yadda Ƙungiyar Gamayyar Ƙasashen Afirka ta ECOWAS ta ja bakinta ta tsuke game da maganar rufe bodar ƙasar Ghana. Abinda a cewar 'yan Kasuwar ya zama tamkar hawan ƙawara ne a kan dokar nan da ta ba wa duk 'yan Afirka  'yancin zirga-zirga a ko'ina a Afirka.  Shugaban ƙungiyar 'yan kasuwar Nijeriya mazauna ƙasar Ghana (NUTAG), Mista Chukwuemeka Nnaji, shi ya bayyana haka a wata tattaunawa ta wayar tarho da ya yi da kamfanin dillancin labarai (NAN), ranar…
Read More