Gobarar gas ta janyo asarar rayuka biyar da dukiyoyi a Abuja

Daga AMINA YUSUF ALI

Aƙalla mutane biyar ne har da yara guda uku suka samu munanan raunuka da kuma shaguna da suka ƙone a sakamakon fashewar silindar gas wacce ta fashe ta tasar da gobara a unguwar Gwagwalada da ke Birnin Tarayyar Abuja. 

 Al’amarin ya faru ne a wani kango kusa da unguwar Dagiri wacce ke kusa da titin Abuja/Lokoja da ke unguwar Gwagwalada a Abuja.  

Shaidun gani da ido sun bayyana wa majiyarmu cewa, a take aka garzaya da majikkatan i zuwa asibitin Zamad da yake a yankin Dagari a Gwagwalada.

Hakazalika, shaidun sun bayyana cewa, musabbabin gobarar shi ne wani mutum da ya zo sayen gas ɗin ya yi kiran waya. Hakan shi ya jawo afkuwar lamarin. 

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *