Bankin Sterling zai fara gudanar da banki maras kuɗin ruwa

Daga AMINA YUSUF ALI

Bankin Sterling ya samu sahalewar Babban bankin Nijeriya, CBN a kan ya rikiɗewa ya koma kamfanin dillancin wasu kamfanonin. Kuma sannan ya buɗe sashen soma tafiyar da harkar banki mara kuɗin ruwa. Wanda ya laƙaba wa sunan, Alternative Bank Limited.

A yanzu dai Bankin ya samu wannan lasisin daga CBN inda Babban Banki ya ba da lasisi a bisa wasu tsararrun dokoki da ya gindaya wa Bankin Sterling ɗin, kamar yadda jaridar Premium Times ta rawaito a ranar Larabar da ta gabata.

Inda Bankin Sterling ya koma tsarin kamfanin dillancin wato ‘holdco’, hakan zai ba da dama ga sauran kamfanonin da suke da alaƙa da shi su zuba hannun jari kuma ya tafiyar da harkokin shugabanci a bankin ba tare da hakan ya shafi al’amuransu na yau da gobe ba. 

Tsarin zai kasance mai kiyaye masu zuba jari daga haɗarurruka da ka iya afkuwa. Amma ba zai ɗauki asara ba idan matsalar ƙin biyan bashin mutane ba ce. 

Sashen tafiyar da banki mara kuɗin ruwa, wato Alternative Bank Limited, aikinsa shi ne ƙulla alaƙar yin kasuwanci tsakanin kamfanoni da kamfanoni ko kamfanoni da mutane da samar wa mutane hanyoyin samun arziki da dogaro da kai. Kuma alaƙar kasuwancin za ta kasance cikin tsarin da ya dace da kuma bin dokokin addini. 

Yadda al’amarin ya kasance dai Bankin Sterling ya ƙulla alaƙa da kamfanin GTCO, babban kamfanin ba da rance a Nijeriya. Kuma Sterling ɗin shi ne banki na biyu da ya rikiɗe ya koma kamfanin dillanci ‘holdco’ a cikin shekarar nan ta 2021. 

A halin yanzu ma dai an fara sayar da hannun jarin Bankin Sterling ɗin a jihar Legas. Zuwa Larabar da ta gabata ma, an saye kaso 2.05 na hannun jarin.

Sauran bankunan da suka daɗe da shiga harkar sun haɗa da Bankin First Bank (ya koma FBN Holdings) da kuma Bankin FCMB sai kuma bankin Stanbic, ya koma (Stanbic IBTC Holdings) yayin da shi kuma bankin Access yake kan hanyar shiga harkar.