14
Jan
Daga AMINA YUSUF ALI Ministar Harkokin Jinƙai, Agaji da Inganta Rayuwa, Sadiya Farouq, ta bayyana jaje ga ‘yan kasuwar da gobara ta lashe wa dukiya a Babbar Kasuwar garin Guru a Jihar Yobe. Gobarar ta yi sanadiyyar ƙonewar sama da shaguna 300 tare da lalata dukiyar miliyoyin naira a ƙarshen makon da ya gabata. Hajiya Sadiya ta bayyana asarar da cewa babba ce, yayin da kuma ta umarci Hukumar Kai Agajin Gaggawa ta Ƙasa (NEMA) da ta gudanar da binciken gani-da-ido kan ibtila'in domin a san yawan asarar da aka yi. Ta ce, “Ina miƙa saƙon jaje ga gwamnatin Jihar…
