Kamfanin ExxonMobil ya jawo mana asarar biliyan 11 – Masuntan Akwa-ibom

Daga AMINA YUSUF ALI

Masunta a jihar Akwa-ibom sun koka a kan asarar Naira biliyan 11 da ta riske su. Inda suka ɗora zarginsu kacokam akan wani Ba’Amurken kamfanin komai da ruwanka na fetir da gas dake jihar. Inda suka ce ya yi buris da buƙatarsu da suka nemi ya biya su diyyar varin man fetur da kamfanin ya jawo. Wanda ya afku a tsakanin shekarar 1998 zuwa 2012.

Masuntan sun bayyana cewa, bayan al’amarin ya faru, sun kai ƙara kotu. Amma ban-bakin da aka yi musu da fatan za a sulhuta a samu maslaha, ya sa suka janye ƙararsu daga kotu, amma sai abin ya ci tura. Har a yanzu da aka shafe shekaru an kasa cimma maslahar. Duk da kuwa a cewar su sun aike da tunasarwa da kuma ƙorafinsu ga mahukuntan kamfanin da kuma masu madafun iko a gwamnati. 

Masuntan waɗanda ‘ya’yan ƙungiyar masunta ta jihar Akwa-Ibom, sun bayyan cewa, ɓarin man fetur ɗin ya faru a tsakanin shekarar 2018 da 2012. Inda ya jawo lalacewar kayan sana’ar tasu ta ‘su’ da kuma durƙushewar masu sana’ar. 

Ƙungiyar ta gudanar da wata zanga-zanga  a watan Yulin wannan shekarar ta 2021 kan nuna alhininsu a kan yadda kamfanin ExxonMobil  ya ƙi biyan su diyyar asarar da suka yi ta Naira biliyan 11 har na tsahon shekaru 14.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *