Amfanin bagaruwa a jikin iyali

Daga BILKISU YUSUF ALI

Tambaya : Salam Anti Bilkisu. Barka da wannan lokaci. Don Allah muna son a yi mana bayanin amfanin Bagaruwa ta Hausa a jikin ɗan’adam.

Amsa: Bagaruwa tana da matuƙar amfani ƙwarai ga lafiyar iyali tana warkar da larurori da dama in har an yi amfani da ita yadda ya dace. Bagaruwa tana da zafi ƙwarai don haka masana kiwon lafiya suke faɗin ake amfani da ita kaɗan-kaɗan ba a son a fiye amfani da ita ko kuma a jima a na amfani da ita musamman a bin da ya shafi sha.

Daga cikin amfanin bagaruwa akwai:-

*Bagaruwa tana da amfani ga mata musamman wadda ta haihu da yawa ko ta buɗe. Bagaruwa na taimakawa ƙwarai wajen haɗe ta. Ana amfani da ita ita kaɗai a gyara ta a fitar da datti da ƙura sai a dake ta ta yi laushi sosai. A riƙa ɗiba kaɗan-kaɗan ana zubawa a ruwan zafi ko a tafasata a ruwan. Za a ke shiga tamkar yadda mai jego ke yi amma a tabbata ruwan ba wanda zai cutar ba ne. A ke yin haka ko da sau biyu a sati ne har a samu biyan buƙata.

*A irin wannan tsarin na sama shi ma ana iya amfani da shi amma ta wani ɓangaren na daban, amma shi kuma ba shiga za a yi ba. Za a ke barinsa a buta ne ana yin tsarki da shi. In son samu ne ya kasance duk lokacin da za a kama ruwan ya zamana ruwan yana da zafi amma ba zafi wanda za a ƙone ba.

*Duka waɗannan hanyoyin guda biyu bayan gyara mace ya matse ta yana kuma kashe kwayoyin cuta da maganin sanyi na ɗauka in an haɗa da ɗan lalle kaɗan da gishiri. Ana iya kama ruwa ko a shiga.

*Ga masu matsalar dafewar haƙori ko warin baki a samu bagaruwa kaɗan da kanumfari a haɗe su ana iya ƙara gawayi da ɗan gishiri amma in ana buƙata. Za a ke goge baki da shi sau biyu a rana. Zai gusar da warin baki ya fitar da datti sannan ya sa haƙori ya yi haske, hatta masu amosanin haƙori zai taimaka musu.

*Ana iya yin asiwaki da icen bagaruwa don magance amosanin haƙori da dafewar haƙori, ana amfani da asiwakin in za a kwanta bacci da lokacin da aka tashi.

*Yana daga cikin larurorin da su ke damun maza a zamantakewarsu da iyalansu shi ne saurin kawowa wanda wannan matsalar tana shafar zamantakewar iyali sosai. Ga namijin da yake da wannan matsalar yana iya samun ‘ya’yan bagaruwa ya tsaftace su ya dake su su yi laushi sosai yake ɗiban kaɗan yana zubawa a cikin ruwa ko madara yana sha. (kaɗan ake sha ba a so a sha da yawa)

Za mu ɗora a lokaci na gaba in sha Allah.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *