Gobarar shagon Next: Hukumar FEMA ta ƙaryata Pantami

Daga AMINA YUSUF ALI

Duk da yaɗuwar hotuna da bidiyo a shafukan yanar gizo da suke nuna cewa, mutane suna ta jidar kaya a yayin da wutar gobara take lamushe wani ɓangare na rukunin shagunan Next a Abuja, inda har ma daga bisani aka ga bidiyon Ministan Sadarwa, Sheikh Ali Isa Pantami, yana zubar da hawaye bisa takaicin yadda mutane suka riƙa satar kayayyaki a shagon, amma duk da haka Hukumar Bayar da Agajin Gaggawa ta Tarayyar Nijeriya (FEMA) ta ƙaryata wancan batu na cewa masu kwasar kayan nan da ake ta yaɗa hotunansu ɓarayi ne.

Wannan batu dai ya fito ne daga bakin Alhaji Abbas Idriss, Darakta Janar na hukumar FEMA, inda ya bayyana hakan ne a wani jawabi da ya yi a ranar Lahadin nan da ta gabata. 

Darakta Janar ɗin ya bayyana wa kamfanin dillancin labarai (NAN) cewa, waɗannan bidiyon  da ake ta yaɗawa na ma’aikatan shagon ne a yayin da suke ta ƙoƙarin ganin sun ceto kayan daga gobarar wacce ta ke barazanar lamushe komai.

A cewar sa, jami’an nasu na FEMA suna dira, suka fara aikin kashe gobarar ba tare da vata lokaci ba. Don haka a cewar sa, ba wani zancen sata da aka yi, duk ƙarya ce ake ta yaxawa a shafukan yanar gizo.

Ya ce: “Abinda kuka gani a bidiyon ma’aikatan rukunin shagunan Next ɗin ne suke ta ƙoƙarin fitar da kayan shagon, amma ko tsinke ba wanda ya fice da shi daga farfajiyar shagon”.

A cewar Idriss, hukumar FEMA da sauran hukumomi kamar Jami’an hukumar kashe gobara NNPC, Rundunar jami’an tsaro na farin kaya, hukumar NEMA, Julius Berger da sauransu duk sun samu kiran gaggawa game da gobarar. Inda kuma suka zo kowa ya ba da gudunmowa aka kashe gobarar.  

Daga ƙarshe ya ba da tabbacin cewa ba a rasa rayuka ba, kuma ba wanda ya jikkata a sanadiyyar wannan gobara. Sannan kuma hukumomin sun yi ayyukansu yadda ya kamata har aka kai gobarar ƙasa.

Sannan ya yi kira ga sauran ‘yan kasuwa da su zama masu taka-tsan-tsan da lamurra domin kauce wa afkuwar gobara. 

Idan mai karatu yana bibiyar lamurra, ba zai kasa sanin wata gagarumar gobara ba da ta afku a rukunin shagunan sayayya na Next ba a garin Abuja, inda har ma mutane suka dinga yaɗa bidiyon yadda wasu suka dinga jidar kaya daga shagunan a lokacin da gobarar take ci.

Abinda ya jawo tofin alatsine ga waɗancan mutane da ake tsammanin sun sace kayan ne. Abinda har ya jawo hankalin malamin addinin Islama kuma ministan Sadarwa, Sheikh Pantami, har ya zubar da hawaye tare da kuka wiwi a masallaci kan yadda al’umma suka lalace da rashin imani; ana gobara su kuma sun ƙoƙarin yin sata.