*Sauya manyan hafsoshin tsaro
*Saudiyya ta kaɗo ’yan Nijeriya daga ƙasarta
*Satar ɗaliban makaranta
*Rufe Masallacin Sheikh Abduljabbar
*Mutuwar Shekau
*Rufe manhajar Tuwita
*Kama jagoran IPOB, Nnamdi Kanu
*Wanke Sheikh El-Zakzaky a kotu
*Kifewar kwale-kwale a wasu jihohi
*Munanar hare-haren ’yan bindiga
*Kasafin 2022
Daga MAHDI M. MUHAMMAD a Abuja
Shekara ta 2021 ta zo ƙarshe, kuma ɗaya daga cikin abubuwan da za a iya cewa kanta shi ne, shekarar cike ta ke da al’amura masu kyau da munana da suka afku.
Batutuwa kamar yaƙi da annobar Korona da al’ummomi a ƙasashen duniya suka ƙagara su ga bayanta da kuma rikice-rikicen ’yan Boko Haram da ISWAP, ’yan bindiga da kuma rikata-rikitar siyasa sun mamaye yawancin kwanakin shekarar.
Bisa ga dukkan alamu, shekarar 2021 ta zama abar ban tsoro. Za a tuna ta a matsayin shekarar ƙunci. Hatta Shugaban Nijeriya Muhammadu Buhari ya yi ishara da hakan a saƙonsa na Kirsimeti da ƙarshen shekara, inda ya ce, shekara ce ta ƙalubalen tsaro da ba a taɓa samun irinsa ba.
Shekarar 2021 ta zo da ƙalubale da ’yan Nijeriya, kamar sauran ƙasashen duniya, tun daga matsalar tsaro da tattalin arziki, hauhawar farashin kayayyaki da kuma annobar Korona, wadda ta qara dagula al’amura a ƙasar. A Nijeriya al’amura da dama sun faru kamar haka:
Sauya manyan hafsoshin tsaro:
Shekarar 2021 ta fara da nasara ga sojojin saman Nijeriya, inda a ranar 1 ga Janairu suka kai wasu hare-hare ta sama kan wani sabon sansanin Boko Haram da ke garin Mana Waji na Jihar Borno. Dakarun sun samu nasarar kisan gomman ’yan ƙungiyar. Sai dai bayan mako biyu ƙungiyar ISWAP ta kai wani samame kan sansanin sojojin Nijeriya a Marte, kuma ta ce, ta kashe sojoji bakwai tare da kama ɗaya.

Kwana 10 da afkuwar haka, Shugaba Muhammadu Buhari ya sauke hafsoshin sojin ƙasar, inda Laftanar Janar Ibrahim Attahiru ya maye gurbin Lafatanar Janar Tukur Yusuf Burutai a matsayin babban hafsan sojin Nijeriya, waɗanda aka jima ana cece-kuce kan barin su a muƙamansu, duk da cewa, wa’adinsu na aiki da na shekaru tuni sun cika. Sai dai a watan Mayu ne sabon babban Hafsan Sojin Ƙasa na Nijeriya, Laftanar Janar Ibrahim Attahiru, ya rasu sakamakon haɗarin jirgin saman soji a Kaduna. An kuma maye gurbinsa da Manjo Janar Farouk Yahaya.
Saudiyya ta kaɗo ’yan Nijeriya daga ƙasarta:
A watan na Janairu ne ƙasar Saudiyya ta taso ƙeyar ’yan Nijeriya kusan 400 daga cikin fiye da 800 da ke tsare a gidajen yarin ƙasar. An killace su kafin a mayar da kowa jiharsa.
Satar ɗaliban makaranta:
An shiga tashin hankali a Nijeriya a 2021, inda ’yan bindiga suke satar ɗaliban makarantar sakandare, musamman mata. A ranar 24 ga watan na Fabrairu ne ’yan bindiga suka yi awon gaba da ’yan makarantar mata ta garin Jangebe da ke jihar Zamfara su fiye da 400, kafin daga baya aka kuɓutar da su. Wannan na zuwa yayin da ake ƙoƙarin kuvutar da ɗaliban makarantar sakandiren Kagara da malamansu da ’yan bindiga suka sace a jihar Neja a ranar 17 ga Fabarairu. A ranar 27 ga Fabrairu aka sako ɗaliban Kagara da malamansu da ma’aikata guda 41 da ’yan bindiga suka sace.

A watan Maris ne masu garkuwa suka yi awon gaba da ‘yan makarantar koyon aikin gona da ke Mando Kaduna su 30. A ranar 20 ga Afrilu ne kuma ’yan bindiga suka yi garkuwa da ɗalibai 20 da malamai 2 na jami’ar Greenfield University da ke Kaduna. A ƙarshen watan na Mayu, wasu ’yan bindiga suka yi garkuwa da ’yan makarantar Islamiyya a garin Tagina da ke jihar Naija.
A ranar 26 ga Yuni Jihar Kebbi ta fuskanci nau’in farko na satar ’yan makaranta, inda ’yan bindiga suka kutsa makarantar gwamnatin tarayya da ke Birnin Yauri suka yi garkuwa da ’yan mata fiye da 30, bayan kashe ɗan sanda guda sakamakon fafatawa da suka yi. A farkon watan Yuli, Nijeriya ta sake yin aramgama da labarin sace ɗalibai fiye da 100 na makarantar sakandare ta Bethel Baptist da ke qaramar Chikun a Kaduna.
A farkon watan Nuwamba ne wasu ’yan bindiga su fiye da 50 suka girgiza birnin tarayya Abuja, bayan sun kutsa rukunin gidajen malaman jami’ar ta Abuja suka kwashi ma’aikatan jami’ar da ‘ya’yansu su shida.
Rufe masallacin Sheikh Abduljabbar:
Labarin ya ja hankali a Nijeriya musamman a arewacin ƙasar shi ne na rufe masallacin Sheikh Abduljabbar da Gwamnatin Jihar Kano ta yi bisa zargin ɓatanci ga Annabi Muhammad (SAW) da kuma tunzura al’umma, wani abu da ya sa shehun malamin da gwamnatin Ganduje yin musayar yawu.

Lamarin ya kai har aka gudanar da muƙabala tsakanin Sheikh Abduljabbar Nasiru Kabara da wasu malamai a Jihar Kano ranar Asabar, 10 ga watan Yulin 2021 wadda gwamnatin jihar ta shirya. Ranar Juma’a 16 ga watan Yuli ne gwamnatin jihar Kano ta gurfanar da malamin a gaban kotu bisa zargin vatanci ga addini da kuma tunzura jama’a, zargin da ya sha musantawa.
Mutuwar Shekau:
Labarin da ya faranta ran hukumomi da ’yan Nijeriya shi ne na kisan-kai da shugaban Boko Haram, Abubakar Shekau ya yi inda rahotanni suka ce ya tashi bam ɗin da ke jikinsa bayan da abokan adawa na vangaren ISWAP suka kutsa dajin Sambisa inda suka nemi tursasa masa yin mubaya’a.
A cikin wani sautin wata wanda kamfanonin dillancin labarai suka samu a watan Yuni, ƙungiyar ISWAP ta ce, Shekau ya mutu ne a lokacin da ya kunna abin fashewa a jikinsa bayan karawa tsakanin ƙungiyoyin biyu.
A sautin, wanda ba a san lokacin da aka naɗe shi ba, wata murya da ake tunanin ta shugaban Iswap Abu Musab al-Barnawi ce, ta ce, “ya kashe kansa nan take ta hanyar kunna abin fashewa”.
Mayaƙan Iswap sun gano shugaban qungiyar Boko Haram ɗin ne kuma suka ba shi damar tuba ya koma cikinsu, a cewar al-Barnawi. “Shekau ya gwammaci ya tozarta a lahira da ya tozarta a duniya,” a cewarsa.
A ranar 25 ga watan Afrilun ne kuma wasu ‘yan ƙungiyar Boko Haram sanye da kakin soji suka yi wa sojojin Nijeriya kwantan-ɓauna, a garin Mainok mai nisan kilomita 36 daga Maiduguri babban birnin jihar Borno, inda suka kashe soji 33.
Rufe manhajar Tiwita:

A farkon Yuni ne kafar sada zumunta ta Twitter ta haɗu da fishin gwamnatin Nijeriya, bayan da kamfanin ya goge wani sako cikin jerin sakwannin da shugaba Muhammadu Buhari ya wallafa a shafinsa inda yake gargaɗin ‘yan awaren IPOB. Kuma har kawo yanzu gwamnatin ba ta buɗe shafin ba, wani abu da ke sa ’yan ƙasar da suka damu da shafin yin zagaye domin amfani da shi.
Kamo jagoran IPOB, Nnamdi Kanu:
Shugaban ƙungiyar IPOB da ke son ɓallewa daga Nijeriya, Nnamdi Kanu ya zo hannun hukumon Nijeriya a ƙarshen watan Yuni duk da cewa gwamnatin Nijeriya ba ta faɗi ƙasar da aka cafke shi ba. An gurfanar da shi a gaban kotu kuma hukumomin Nijeriya na ci gaba da tsare shi.

Kanu yana fuskantar zarge-zargen da suka shafi cin amanar ƙasa lamarin da ya sa aka gurfanar da shi a gaban wata babbar kotun tarayya da ke Abuja bisa fafutukar da yake yi wajen ganin an kafa ƙasar Biafra ta hanyar IPOB.
Wanke Sheikh Ibrahim El-Zakzaky a kotu:
A ƙarshen watan na Yuli ne wata babbar kotu da ke zama a Kaduna ta wanke Jagoran Harkar Musulunci a IMN, Sheikh Ibrahim Elzakzaky da mai ɗakinsa daga laifukan da ake tuhumarsu.
Babbar Kotun Jihar Kaduna ta bayar da umarnin a saki Sheikh Ibrahim El-Zakzaky tare da matarsa Zeenah Ibrahim, inda ta wanke su daga dukkan zargin da ake yi musu.

A cewar lauyan Zakzaky, Barista Sadau Garba, kotun ta wanke su daga zargi takwas da gwamnatin Jihar Kaduna ta gabatar. Hakan ne ya kawo ƙarshen zaman mutanen biyu a tsare har na kusan shekaru shida kan laifin da ba su aikata ba.
Kifewar kwale-kwale a wasu Jihohi:
Wani labarin marar daɗi da ya faru a watan Mayun 2021, shi ne na yadda wani kwale-kwale ɗauke da fasinjoji fiye da 150 a jihar Kebbi ya nutse, al’amarin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutum kusan 150. Mutanen dai ‘yan kasuwa ne da ke kan hanyarsu ta dawowa daga cin kasuwa a makwabciyar jihar Neja.
A watan Nuwamba ne kuma wani kwale-kwalen fasinja a ƙaramar hukumar Ɓagwai da ke jihar Kano, ya nutse da fasinjoji, inda kusan 30 suka mutu ciki har da ƙananan yara ’yan makarantar Islamiyya.
Munanan hare-haren ’yan bindiga:
A watan Oktoba ne kuma wasu ‘yan bindiga suka buɗe wuta irin ta mai kan uwa da wabi a kan masallata yayin da suke sallar Asubahi, a garin Mazakuka da ke jihar Neja kuma nan take mutum 17 ciki har da limamin suka rasu.
A watan ne wasu da ba a iya tantance ko suwa ne ba suka dasa bam a layin dogo da ke tsakanin Abuja zuwa Kaduna, wani al’amari da ya janyo dakatar da zirga-zirgar jiragen na ‘yan kwanaki. Wannan al”amari ya tayar da hankalin fasinjojin da suka ƙauracewa bin hanyar mota daga Abuja zuwa Kaduna.

A watan Nuwamba, rundunar sojin Nijeriya ta tabbatar da cewa mayaaan ISWAP da ke ikirarin jihadi a yammacin Afrika sun halaka Birgediya Janar Dzarma Zirkushu da wasu sojoji uku, a lokacin da suka je kai ɗauki yayin wata ba-ta-kashi da mayaƙan.
A watan Disamba ne gungun matasa a arewacin Nijeriya a jihohi daban-daban suka gudanar da zanga-zangar kiraye-kiraye ga gwamnatin Nijeriya ta ɗauki matakin kawo ƙarshen matsalar tsaro da ke addabar yankin.
Hakan dai ya bito bayan sanarwar da rundunar ‘yan sandan jihar Sokoto da ke arewacin Nijeriyar ta bayar cewa aƙalla mutum 21 ne wasu ’yan bindiga suka ƙona a wata motar fasinja lokacin da suka yi musu kwanton-ɓauna. Za a iya cewa shekarar 2021 ta zamo da ƙalubale ga Nijeriya musamman a sha’anin tsaro.
Hasashe kan shekarar 2022:
Daga dukkan alamu shekara mai zuwa ta 2022 tna iya zama matsi ga Nijeriya. Duba da la’akari da manufofin siyasa wanda suke kan gaba wajen shimfiɗa ginshikin ƙasar zuwa wani yanayi mai haɗari ko kuma taɓarɓarewar al’amura.

A shekara mai zuwa ta 2022, za a samu manyan batutuwa da ci gaba da suka shafi siyasa, tattalin arziki da zamantakewar ƙasarmu, kuma za su buƙaci tsayayyen ƙudurin siyasa da tsarin mulkin da al’umma irin tamu don cimma nasaara. Menene waɗannan batutuwa da ci gaba, kuma ta yaya za su bayyana?
Na farko, siyasa. Ba makawa za a fafata a tsakanin manyan jam’iyyun siyasa biyu na APC mai mulki da kuma jam’iyyar PDP a fili.
A jam’iyyar PDP, batun wanene zai fito takarar shugaban ƙasa a jam’iyyar zai kasance mai cike da cece-kuce kuma zai iya janyo jam’iyyar ta shiga cikin rikici. Gwamna Nyesom Wike na jihar Ribas ya amince da hakan kwanan nan.
A shekarar 2022, jiga-jigan shugabannin Nijeriya za su fuskanci gwaji mafi tsanani na siyasa, tattalin arziki da zamantakewa duk da haka na iyawa da jajircewarsu ba wai kawai su dunƙule ƙasar waje ɗaya ba har ma da tsara wata sabuwar hanya ta gaba. Yadda za su magance wannan ƙalubale zai tabbatar da dacewarsu da rayuwarsu da ta ƙasar.
Kasafin kuɗin 2022:
Yayin da Arewa ke fama da Boko Haram da kuma ‘yan bindiga, a fannin tattalin arziki da kuma inganta rayuwar al’umma ana ƙara yi wa yankin rata da tazara mai yawan gaske.
Irin yadda matasan Arewa ke ci gaba da yin tururuwa zuwa ci-rani a kudancin Nijeriya, hakan na ƙara nuni da cewa tabbas ayyukan bunƙasa rayuwa da kuma matsalolin tsaro na ci gaba da danƙwafar da yankin.
Kasafin kuɗin da jihohin Arewa su ka yi na shekarar 2022, ya zama ma’aunin auna irin nauyin koma-bayan da yankin ke ciki, kuma hakan na nufin babu rana, shekara ko lokacin shawo kan lamarin.
Yayin da Jihar Legas ta yi kasafin 2022 na abin da za ta kashe a shekarar har naira tiriliyan 1.758, ita kuwa Jihar Kano da ake wa kallon cibiyar kasuwanci a Arewa, kasafin naira biliyan 196 kacal ta yi. Wato Legas ta nunka Kano kasafi sau takwas kenan.
Abin mamaki shi ne yadda Jihar Katsina ta fi Kano yawan kasafin 2022. Katsina za ta kashe naira biliyan 340.9.
Haka nan jihar Kaduna ta fi Kano yawan kasafin 2022. Kaduna za ta kashe naira biliyan 278.5.
Jihar Barno inda ake fama da matsalar Boko Haram, ita ma kasafin ta na 2022 ya zarce na Kano. Barno za ta kashe naira biliyan 276. Jihar Zamfara naira biliyan 160, Yobe naira biliyan 164, Jigawa naira biliyan 177, sai Sokoto naira biliyan 188.
Idan aka haɗa kasafin jihohin Kano, Katsina, Kaduna, Barno, Zamfara, Yobe, Jigawa da na Sokoto, za a ga jimla za su kashe kusan daidai da abin da jihar Legas za ta kashe ita kaɗai.
Jimlar kasafin jihohin nan na Arewa su takwas, ya kama naira tiriliyan 1.774. Babban abin damuwar kuma shi ne, yayin da akasarin kuɗaɗen da waɗannan jihohi na Arewa za su kashe duk daga aljihun gwamnatin tarayya zai fito, ita kuwa Legas yawancin kuɗaɗen na ta daga kuɗaɗen shigar da jihar ke tarawa ne.
Wanann ya nuna cewa, jihohin Arewa ba su da wani kataɓus na dogaro da kai, sai dai kawai su dogara da kuɗaɗen fetur da gwamnatin tarayya ke rabawa a kowane ƙarshen wata.
