Mu gamu ranar Asabar mu huta

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Duk da dama a tsarin aikin gwamnati a Nijeriya ranar Asabar ranar hutu ce ta ƙarshen mako, hakan bai hana zuwan wani hutun a ranar hutu ba cikin ikon Allah, wato Asabar ɗin nan ce ɗaya ga watan Janairun sabuwar shekarar miladiyya 2022. In za a tuna ai a makon da ya gabata ma an gudanar da bikin Kirsimeti na mabiya addinin Kirista a ranar Asabar.

Haƙiƙa la’akari da hutun ranakun biyu ya faɗo a ranar hutu shi ya sa ministan cikin gida na Nijeriya Rauf Aregbesola ya matsar da hutun zuwa ranakun aiki. Wato an huta Litinin da Talata wato 27 da 28 don Kirsimeti da wannan shekaren Kirsimeti da a turance a ke kira ‘Boxing Day.’ Hakanan shi ma hutun na sabuwar shekara a ka matsar da shi zuwa litinin 3 ga watan janairu. Don haka na ke cewa mu haɗu ranar Asabar don mu huta, in hutu ya shiga jiki har runtsawa za ka an yi a samu barci na wani lokaci.

Sai dai kash shin hutun nan na gudana ta hanyar runtsawa da ido biyu rufe?, e kuma a’a. Ga a na iya samun hakan a irin birane daf da fadar gwamnati kamar Abuja da sauran manyan birane da ke da wutar lantarki da jami’an tsaro. Ga a’a kuma barcin da wuya ya samu da minshari a irin su Sabon Birni a jihar Sokoto, Shinkafi a jihar Zamfara, Birnin Gwari a jihar Kaduna da Mashegu a jihar Neja. Wannan shi ke nuna ƙalubalen tsaro da ya zama kusan ruwan dare musamman a yankin Arewa maso yammacin Nijeriya.

Duk rediyon da ka kunna ko talaibijin da ka kalla ko jarida da ka karanta da ma yanar gizo in ka hau, za ka ci karo da labarun an yi kisan gilla kan talakawa a gari kaza ko an sace mutane a gari kaza ko miyagun iri sun buɗe wuta kan matafiya a hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Lamarin nan fa kamar almara ko hikiyoyin Shehu Jaha amma an wayi gari ya zama gaskiya. Zai yi wuya ka tara mutum biyar ka tambaye su yaya lamuran tsaro, ba su ba ka labarin an taɓa sace wani na su ko abokin su ko ma hakan ya kai ga rasa rai. Ni kai na da na ke rubutun nan an taɓa kama kani na a wajen yankin Birnin Gwari amma cikin ƙaddara ya nemi artabu da ɓarayin su ka yi ma sa kisan gilla. Hakanan a lokacin da Boko Haram ke da zafi, wani bom ya tashi a tashar Daɗin Kowa a Gombe inda ya rutsa da wani ɗan uwana wanda direba da kan yi lodi a tashar.

Mutane da dama su na da irin wannan labara da za su bayar ko ma wanda ya fi shi tsanani. Wasu labarun ma ga mari ne ga tsinka jaka, Miyagu su yi kisan gilla su yi fyaɗe kai su ma banka wa ƙauyuka wuta ko ƙona mutanen da ƙaddara ta hau kansu. Sau da dama za ka ji miyagun na cewa ai su ma zalunci a ka yi mu su, shi ya sa su ka ɗauki makamai don zaukar fansa kan mai uwa da wabi.

Haƙiƙa ba adalci ba ne a rama zalunci da zalunci. Aƙalla ko a littattafan addini an yi bayanin yanda a kan rama cuta daidai gwargwadon cutarwa da a ka yi wa mutum. A irin wannan ramuwa a kan tsaya a iya kimanin abun da a ka rasa ko zaluncin da a ka yi? Shin a kan yi ramuwar a kan waɗanda tun farko su ka yi zaluncin ko dai kawai duk wanda tsautsayi ya faɗa kan sa shikenan ya zama nama?

Mamaki kan kama ni ainun in na ji yadda a kan yi cinikin wanda a ka sace da fara buƙatar Naira miliyan 100! Shin masu satar nan sun ɗauki Naira miliyan 100 a matsayin Naira dubu 100 ne? Alamu na nuna haka.

In kuma ba haka ba ne wuce gona da irin ya kai iyaka. A ina mutum zai nemo Naira miliyan 100 a yanayin ƙuncin tattalin arzikina nan. Wani ba shi gida ko gona da zai sayar ya rage hanya kan kuɗin fansa amma sai ka ji a na buƙatar a kawo miliayan 100 har ma da haɗawa da barazanar kisa ko azabtarwa matuƙar ba a kawo kuɗin ba.

In tunanin ɓarayin nan haka jama’a ke da ikon samun kuɗi da ya kamata yau ba almajiri ko ɗaya a titunan arewacin Nijeriya. Ya kamata da ba za a samu gidan da su ke kwana da yunwa ba. Tsanantar talauci fa kan sa mutum na da ciwo a jikin sa amma in ba ya kwantar da shi ba ne sai ka ga ya cigaba da lallaɓawa don neman na kalaci. Wato ma’ana yau in mutum ya shiga asibiti a ka haɗa shi da kuɗin gwaje-gwaje kaɗai sai gumi ya yanko ma sa.

Hakan kan sa wasu su ke gagara zuwa a riƙa bincika lafiyar su don sanin zafin jini, ciwon suga, ciwon hanta, zazzaɓin cizon sauro da sauran su. In ba fahimce ni ba, yau gwamnati ta ware wani asibiti ko wata ƙungiya mai zaman kan ta ta ayyana yi wa mutune gwajin cutuka kyauta ka ga yawan mutane da za su yi tururuwa don a duba su. Ai kawai mutame na rayuwa ne cikin matsaloli inda sai an lura za a gane abin da ke damun su.

Idan ɗan uwa ka na son gwadawa kuma in Allah ya sa ka na da Naira dubu 10 kacal ka raba ta gida goma ka je garin ku a karkara ka shiga gidajen makwabta 5 hagu 5 dama ka gaishe su ka ba da Naira dubu 1 a kowane ka ga irin fatar alheri da za a yi ma ka. Ƙalubalen ya zama biyu a wasu sassa, ga ƙuncin tattalin arziki ga rashin tsaro. Duk inda waɗannan abubuwa biyu su ka yi katutu to mutane a firgice su ke dare da rana.

A wannan shekara ta 2022 akwai abubuwa da yawa da al’ummar Nijeriya ke fatar su zo mu su da sauƙi don lokacin zuwan abubuwan ya yi. Kaɗan daga waɗannan lamura sun haɗa da shirin qara farashin man fetur, fara zafafar siyasar babban zaɓen 2023 da gwagwarmayar masu hangen nesa na hana tsinka dangantakar Hausa-Fulani.

Ga ƙarin farashin man fetur zai zama ba makawa matuƙar gwamnati ta kammala janye tallafin man inda dama an shiryawa mutane su san lita za ta kai Naira 320-340. In hakan ya faru kuwa wato karin fiye da kashi 100% kayan masarufi za su yi tashin ba na gauron zabi ba har ma jirgin ledar wasan yara.

Yanzu ma yaya lafiyar kura bare ta yi takalmi. Kullum ka je kasuwa sai ka ji ƙarin farashi da a ka samu. Damuwar ita ce akasarin mutan Nijeriya talakawa da ke rayuwa da samun kasa da ma’aunin talauci wato dala 1 a wuni a yanzu wajen Naira 565 kenan.

A birni dai Naira 565 ba za ta saya ma ka kyakkyawar marar tuwo ba sai dai shinkafa garau-garu haɗe da nama jani-in-ja-ka. Ga lamuran siyasa kuma irin wannan lokaci ya na da na sa tsautsayi na ɗaukar kowane mataki kan abokan hamaiya a kowace jam’iyya daga ‘yan siyasar ko a mutu ko a yi rai. Gaskiya har yanzu bangar siyasa ba ta kare ba a ƙasar nan.

A wasu sassan ma ‘yan bangar sun zama ‘yan ta’adda. Yo ‘yan ta’adda ma na tun da za a iya tura su su kai farmaki kan abokan hamayya. Sai kuma batun guguwar da ke neman raba Hausa-Fulani da ke daurowa a arewar-arewa.

Na ga yadda wasu ke bari hushi na ɗaukar su, su na kanbama wannan tsinka dangantaka a yanar gizo musamman don ganin waɗanda a ke samu da satar mutane Fulanin daji ne. Hakika in mun ɗauke su a matsayin Fulani kai tsaye don dangin masu magana da harshen Fulatanci ne ba za mu dau matsaya mai ma’ana ba. Shawara a nan a ɗauki ‘yan ta’adda da sunan su ko miyagun iri da sunan su miyagu. Mugu za a iya samun sa a tsakanin kowace irin al’umma.

Ka ai ko lokacin Boko Haram ba a ce Kanuri ko Barebari na kashe mutane da sunan addini ba, amma sai a ka laƙabawa masu kisan gilla ba hurumin shari’a da ‘yan ta’adda ko ma inkiyarsu Boko Haram. Wannan fa babbar matsala ce da sai an kai zuciya nesa za a fahimci lamarin. Me zai saura a arewacin arewa in an tsinka ‘yan uwantakar Hausawa da Fulani?