Kasuwanci

Ɓacin rana: Attajiri Elon Musk ya tafka mummunar asara a dukiyarsa

Ɓacin rana: Attajiri Elon Musk ya tafka mummunar asara a dukiyarsa

Daga AMINA YUSUF ALI Attajirin Biloniyan nan, Elon Musk ya tafka mummunar asara har ta zunzurutun kuɗi, Dala Biliyan 25 a cikin kwana guda rak! Wato dai kamar yadda Hausawa kan ce, 'wai ba kullum ake kwana a gado ba'. Al'amarin haka yake, domin Duniya juyi-juyi ce; watarana zuma, watarana kuma maɗaci. Wannan shi ne yadda za a fasalta al'amarin da ya wakana ga wannan attajiri Elon Musk. Mutumin da ya fi kowa arziki a faɗin Duniya. Al'amarin ya faru ne sakamakon rashin samun kasuwa da attajirin ya yi a ƙoƙarinsa na sanya hannayen jarin kamfanin ƙera motocin nan na…
Read More
Kifin ƙanƙara: Gwamnati ta ba mu lambar yabo kan tsaftar sana’armu – Sani Lawan Sani

Kifin ƙanƙara: Gwamnati ta ba mu lambar yabo kan tsaftar sana’armu – Sani Lawan Sani

Daga BABANGIDA GORA a Kano Sana'ar kifi mai ƙanƙara sana'a ce da ma fi akasari ba Hausawa ne suke gudanar da ita ba a da, amma a yanzu Hausawa sun yi mata kaka-gida. Wakilin Blueprint Manhaja, Babangida Gora, ya samu zantawa da shugaban ƙungiyar masu sayar da kifi mai ƙanƙara na Jihar Kano, Alhaji Sani Lawan Sani. Ga kuma yadda tattaunawar tasu ta kasance. MANHAJA: Da farko, masu karatu za su so su san waye Alhaji Sani Lawan?SANI: To kamar dai yadda ka faɗa, sunana Alhaji Sani Lawal Sani, kuma ni ne shugaban masu sana'ar sayar da kifi mai kankara…
Read More
Hukumar Kwastam: CBN ya kawo ƙarshen cajin masu safarar kaya ba bisa ƙa’ida ba

Hukumar Kwastam: CBN ya kawo ƙarshen cajin masu safarar kaya ba bisa ƙa’ida ba

Daga AMINA YUSUF ALI Babban Bankin Nijeriya, CBN ya gabatar da wani sabon tsarin da zai hana hukumar Kwastan cajar masu shigowa ko fita da kaya a ciki da wajen Nijeriya ba bisa ƙa'ida ba. CBN ɗin ya ƙaddamar da sabon tsarinsa na 'evaluator' da 'e-Invoice' waɗanda da su ne tsari na yanar gizo da 'yan kasuwa za su dinga amfani da su  don biyan kuɗin shige da fice da kaya ba tare da an yi musu lissafin awon igiya kamar yadda yake faruwa a baya.  Wannan bayani dai ya fito ne daga wata sanarwa da Babban Bankin ya wallafa…
Read More
An buɗe rukunin Kamfanonin RUSBI a Kano

An buɗe rukunin Kamfanonin RUSBI a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano An buɗe rukunin  kamfanonin sarrafa abubuwa daban-daban, Kamfanin mai suna Rufa'i Sule Bichi wato RUSBI wanda mai tallafa wa al'umman nan  Alhaji Rufa'i Sule Bichi ya buɗe, a ranar Talata da ta  gabata a ƙaramar hukumar Kumbotso cikin birnin Kano. Taron ya gudana ne a ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dakta Ibrahim Aminu Tsanyawa. Kwamishina Dakta Tsanyawa ya yi jinjina ga Alhaji Rufa'i Bichi dangane da irin wannan babban yunƙuri, sannan ya yi kira ga masu hali da su yi koyi da irin wannan aiki domin cigaban al'ummar Kano da ƙasa bakiɗaya. Rukunin…
Read More
Abinda ya sa NLNG hana sayar da gas ga ƙasashen waje

Abinda ya sa NLNG hana sayar da gas ga ƙasashen waje

Daga AMINA YUSUF ALI A yanzu haka dai hukumar hada-hadar Gas ta Gwamnatin Tarayyar Nijeriya (NLNG) ta ba da odar hana fita da gas zuwa wasu ƙasashen sai dai a sayar da shi ga dilolin cikin gida. Abinda ya jawo ruguzowar farashin gas ɗin girki ga al'ummar ƙasar.  Wannan umarni na NLNG ya zo ne a dai-dai lokacin da jama'a suke kokawa da yadda farashin gas ɗin ya yi tashin gwauron zabi a ƙasar tun daga watanni biyar da suka wuce.  Hukumar Rarraba gas ɗin ta Nijeriya ta bayyana cewa, ana sa ran nan gaba kaɗan za ta sauko da…
Read More
PAPSS zai rage buƙatar amfani da Dala da Fam a Afirka – Emefiele

PAPSS zai rage buƙatar amfani da Dala da Fam a Afirka – Emefiele

Gwamnan Babban Bankin Nijeriya, CBN, Godwin Emefiele ya bayyana cewa, dandalin hada-hadar kuɗi tsakanin ƙasashen Afirka, PAPSS, zai kawo ƙarancin buƙatar amfani da kuɗaɗen waje a yayin cinikayya tsakanin ƙasashen Afirka. Wato tasirin Dala da Fam har ma da Yuro zai ragu matuqa a yankin na Afirka.  Gwamnan ya yi wannn bayani ne a yayin ƙaddamar da dandalin na PAPSS a garin Accra na ƙasar Ghana a ranar Larabar makon da ya gabata. Bankin safarar kayayyaki na ciki da wajen Afirka, da Bankin Afrexim, tare da haxin gwiwar Cibiyar haɗin kan Afirka (AU) hukumar AfCFTA, su ne suka ƙaddamar da…
Read More
Bankin Standard Chartered zai rufe rassansa a Nijeriya

Bankin Standard Chartered zai rufe rassansa a Nijeriya

Daga AMINA YUSUF ALI A halin yanzu dai ana tsammanin rassa goma sha uku ne daga rassan Bankin Standard Chartered ne za su cigaba da aiki a ƙasar Nijeriya. Hakan ta faru a dalilin yunƙurin bankin na ganin ya rage wasu sassansa da ke ƙasar nan.  Shi dai wannan Rukunin Bankunan na Standard Chartered na Nijeriya yana da Shalkwatarsa ne a birnin Landan ta ƙasar Ingila. Babban banki ne wanda  yake tafiyar da harkokin kasuwancin kuɗi iri daban-daban.  Jaridar Bloomberg ita ta yi wannan rahoto a ranar Litinin ɗin nan da ta gabata. Inda ta bayyana cewa, bankin zai dakatar…
Read More
Nijeriya ta fara nesanta kanta daga amsar rancen Ƙasar Chana – Amechi

Nijeriya ta fara nesanta kanta daga amsar rancen Ƙasar Chana – Amechi

Daga AMINA YUSUF ALI Rahotanni sun bayyana cewa, Nijeriya ta kewaye Ƙasar Chana, inda ta ƙi amsar rancen Dalar Amurka Bilyan 14.4 da ta ke nema, domin gina layin dogo ko digar jirgin ƙasa a kudancin ƙasar.  Jaridar Premium Times ta rawaito cewa, tuni shirye-shirye sun yi nisa daga ɓangaren Nijeriya don neman rancen kuɗin daga bankin Standard Chartered, wanda ɗan asalin Landan ne.  Amma wasu masu rahotannin suna ganin cewa, rashin amsar bashin Chana da Nijeriya ta yi kamar Nijeriya tana neman 'yanta kanta ne daga ɗaurin zargagungun ɗin da ƙasar Chana take shirin yi mata sakamakon ɗimbin bashin…
Read More
’Yan kasuwar Rimi a Kano sun koka kan ruguje rumfunansu

’Yan kasuwar Rimi a Kano sun koka kan ruguje rumfunansu

Daga MUHAMMADU MUJITABA a Kano Wasu 'yan kasuwa da ke kasuwar Rimi cikin ƙaramar hukumar birnin Kano sun koka kan yadda suka wayi garin Talata da labari mara daɗi na cewa jami’an tsaro da wasu da suka ce lauyoyi ne sun bayyana da asubahi Talata, inda suka rushe rumfuna 18 na wani sashi na kasuwar Rimi cikin birnin Kano. Malam Iliyasu Muhammad mai sana’ar siyar da mai a kasuwar ya ce suna zaune a wannan wuri ne tun kimanin shekaru 20 da suka wuce a matsayin sashin rumfunan temfurare wato na wucin gadi, wanda aka basu tun lokacin da aka…
Read More
Ƙasashe 51 sun haramta amfani da kuɗin Kirifto

Ƙasashe 51 sun haramta amfani da kuɗin Kirifto

Daga AMINA YUSUF ALI Duk da irin shuhurar da tsarin samar da kuɗi ta hanyar cinikayyar sulalla ta yanar gizo, wato Kirifto Karansi ko Bit Koyin har yanzu ya kasa samun cikakkiyar karɓuwa a duniya. A halin yanzu bincike ma ya shaida cewa, yawan ƙyamatar Kirifto ya ƙara ninkuwa ne a 'yan shekarun nan ma fiye da duk shekarun baya. Tun a shekarar 2018 ne dai da ma aka samu adadi mai tsoka na ƙasashen Duniya waɗanda suka haramta amfani da tsarin kuɗin a cikin ƙasashensu. Inda jimillar ƙasashen da suka soke Kirifto ɗin suka kai 42 wato bayan da…
Read More