An buɗe rukunin Kamfanonin RUSBI a Kano

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

An buɗe rukunin  kamfanonin sarrafa abubuwa daban-daban, Kamfanin mai suna Rufa’i Sule Bichi wato RUSBI wanda mai tallafa wa al’umman nan  Alhaji Rufa’i Sule Bichi ya buɗe, a ranar Talata da ta  gabata a ƙaramar hukumar Kumbotso cikin birnin Kano.

Taron ya gudana ne a ƙarƙashin jagorancin Kwamishinan lafiya na jihar Kano, Dakta Ibrahim Aminu Tsanyawa.

Kwamishina Dakta Tsanyawa ya yi jinjina ga Alhaji Rufa’i Bichi dangane da irin wannan babban yunƙuri, sannan ya yi kira ga masu hali da su yi koyi da irin wannan aiki domin cigaban al’ummar Kano da ƙasa bakiɗaya.

Rukunin kamfanonin dai suna harkar ƙera ƙofofi da tagogi da gina rijiyoyin burtsatse da harkar gasa burudi da kayan ƙwalan da maƙwalashe, da saye da sayar da kayan noma, da harkar sarrafa amfanin gona da sauransu.

Shugaban Kamfanin kuma wanda ya asssa Kamfanin, Alhaji Rufa’i Sule Bichi, ya gode wa Allah S.W.T da ya ba shi dama da ikon buɗe wannan Kamfani, sannan ya gode wa waɗanda suka halacci wannan addu’a ta buɗe kamfanin.

Shi ma a Jawabinsa, Alhaji Nura Kabir Bichi, ya ce  “Assasa wannnan babban Kamfani da Alhaji Rufa’i Sule ya yi domin kasuwanci da taimakawa al’umma babbar nasara ce ga al’ummar jihar Kano da ma ƙasa bakiɗaya.

Sannan ya ƙara da cewa “Ire-iren wannan kamfani za su taimaka wajen rage aikin yi musamman ga matasa, domin idan ka duba za ka ga cewa akwai matasa da dama da aka ɗiba, kuma ana  shirye-shirye daukar wasu, duka dai don cigaba da tallafawa al’umma” inji Alhaji Nura Bichi.

Taron addu’a da buɗe Kamfanin dai ya samu halartar ɗimbin ‘yanuwa da abokan arziki da ‘yan kasuwa da malamai da  ma’aikatan gwamnati da kuma ‘yan siyasar jihar Kano da ƙasa bakiɗaya.