An nemi ƙungiyoyi a Jihar Sakkwato su cire siyasa a tsakaninsu

Daga AMINU AMANAWA Sakkwato

Shugaban Hukumar Zakka da Waƙafi na Jihar Sakkwato, Malam Muhammad Lawal Maidoki (Sadaukin Sakkwato) shine ya bayyana hakan a lokacin da mambobin ƙungiyar masu kiran kafafen yaɗa labarai ta jihar suka kai ziyara a ofishin hukumar.

Shugaban ya yaba wa ‘ya’yan ƙungiyar akan jajircewar su da kuma gudanar da ayyukan cigaba a cikin al’umma.

Shugaban ya yaba musu akan namijin ƙoƙarin da suka yi na bayar da Tallafin ga ‘yan gudun hijira ta hannun hukumar Zakka da Waƙafi a ‘yan kwanakin nan.

Haka ma shugaban ya janyo hankalin mambobin ƙungiyar da su cire saka siyasa ga dukkan lamurransu mussamman kasancewarsu idanun al’umma kuma suna bayar da gudunmawa wajen kiran kafafen yaɗa labarai a dukkan lamurran da suka shafi ƙasa.

Shugaban ya zayyano ayyukan da hukumar ke gudanarwa a matakai daban-daban, ya kuma nemi mambobi ƙungiyar da su riƙa bai wa hukumar shawarwari a duk lokacin da suka ga inda aka yi ba daidai ba.

Da ya ke mayar da jawabi shugaban ƙungiyar Malam Abdul-Azeez Muhammad Asada, ya yayi godiya a bisa ga tarbar da suka samu daga shugaban hukumar, haka ma ya qara jaddda goyon bayansu akan ayyukan da hukumar zakka ke yi a wannam jihar.

Daga ƙarshe an bai wa mambobin ƙungiyar damar yin tambayoyi da bayar da shawarwari a dukkan bangarorin da hukumar ke gudanar da ayyukanta.

Taron ya sami halartar mambobin ƙungiyar daga sassa daban-daban da kuma daraktocin hukumar Zakka da Waƙafi da wasu ma’aikatan hukumar.