Rashin ƙa’idojin rubutu na jirkita saƙon marubuci – Ibrahim Nayaya

“Akwai tasirin ƙa’idojin rubutu a litattafan Hausa”

Daga AISHA ASAS

Ɗaya daga cikin dalilan da masana su ka ce ya ciyar da rubutun Hausa ko a ce rubutun ‘Adabin Kasuwar Kano’ baya shine, kurakuren da su ka yawaita a cikin littattafan. A na ɗora alhakin wannan kan su marubutan litattafan, saboda kasancewar su ne masu wuƙa da nama a lamarin. Duk da haka, su kansu masanan na da na su kaso a wannan matsala, duba da cewa, da yawa daga cikin marubutan ba masu sani ne a kan Hausa ba. Ko da yake idan aka yi duba da ƙarancin sani kan ɓangaren da suke da shi, za a yaba wa ɗan ƙoƙarinsu, saboda haka fito da hanyoyi masu sauƙin ɗauka da kuma ba su tallafi na lokaci domin gyara ga rubutun tare kuma da sanar da su illolin da ke tattare da rubutu ba ƙa’ida ne zai kawo mafita. Wannan ne ya sa, shafin adabi na Manhaja, ya nemi tattaunawa da ƙwararre a fagen rubutun Hausa, don warware wa masu karatunmu wasu daga cikin matsalolin da ke tattare da kurakuran rubutu da kuma tasirin bin ƙa’idoji a rubutu. Baƙon na mu ba ɓoyayye ba ne. Masu karatu Ibrahim Nayaya ne a shafin adabi na wannan sati, wanda shi ƙwararren marubuci ne kuma masanin ƙa’idojin rubutun Hausa, wanda ya zarce sa’a. A sha karatu lafiya:

Mutane na ganin kurakuren rubutu ne ƙashin bayan rashin tagomashin littafan Hausa a duniya, musamman ma na nan Arewa. Za mu so jin ra’ayinka.
Assalamu alaikum warahmatul Lah. Ba makawa, kurakuren rubutu da suka yi kaka-gida a cikin littattafanmu na Hausa, ka iya su ne ummul-abaisin zagwanyewar daraja da ƙimar waɗannan littattafai; musamman a manyan makarantun da ake nazarin harshen Hausa. Domin da yawa cikin waɗannan littattafai maabotansu ba su ma san waɗannan ƙaidojin ko dokokin rubutun ba, ballantana su bi, amma ba fa wannan ce matsalar kaɗai ba, aa, akwai wasu matsaloli jingim.

Idan ka ɗauki tsarin rubutun Hausa wanda da shi waɗannan marubuta ke rubuta littattafansu, za a iske ƙa’idojin da dokokin sun yi gabas, su kuwa sun yi yamma, maana babu mahaɗa a tsakani, duk da akan sami ɗaiɗaiku suna kwatantawa, suna bin ƙa’idojin rubutun Hausa, amma fa su ne kaɗan. 

Amma idan mu ka koma ga matsalolin da suka haddasa zagwanyewar littattafan Hausa a arewacin ƙasar nan, bai fice abubuwa biyu zuwa uku ba, amma su ɗin ma dole mu jingina su ga rashin bin ƙa’idojin rubutun da ƙarancin fasahar marubutan. Babbar matsalar a fahimta ta, tana da nasaba rashin samun goyon baya daga malaman manyan makarantu zuwa ga su marubutan. Wannan na nufin, malamai a matakan manyan makarantu ba sa ƙaddara littattafan Hausa a matsayin abubuwan da ake buƙata, kamar yadda ba su fiye damuwa da bai wa ɗalibai ayyukan nazari a cikinsu ba. Haka a matakan hukumomin tsara jarrabawar WAEC, da NECO, da kuma NBAIS, dukkaninsu ba sa laakari da waɗannan littattafai, duk dama dai ya dace tun a matakin Hukumar Ilimi ta Ƙasa a ce ta sanya wasu muhimmai cikin waxannan littattafai domin a rinqa nazartarsu, wannan sai ya bayar da dama ga su marubutan su rinqa inganta ayyukansu. Amma bisa kyautata zato da na ke yi, rashin sanya waɗannan littattafai ko maye gurbinsu da waɗanda mu ka taso mu ka gani a cikin manhaja, na da nasaba da rashin bin ƙaidojin rubutun Hausa, da rashin ƙwarewa, da ƙarancin fasaha, duk da fa za a iya tsamo wasu daga cikinsu waɗanda za a iya amfani da su a kowanne mataki.

Har wa yau, akwai matsalar rashin bayar da littafin ga masana domin su duba mu su tare da yi mu su gyare-gyare. Ba na mantawa, a shekarar da aka karrama Malam Ado Ahmad Gidan Dabino da lambar yabon MON, na ziyarce shi domin taya shi murna. Cikin hirar da mu ka yi da shi; yake faɗa min cewa, ya taɓa rubuta wani littafi, sai ya kai wa Farfesa M.K.M Galadanci domin ya duba masa. To idan ka dawo ga marubutanmu na yanzu, da wuya ka ga marubuci ya rubuta littafi sannan ya kai wa wani masani a wannan ɓangare domin ya duba masa, idan ya yi haka yana ganin ya ci baya. Duk da wasu na kafa hujja da cewa, wai malaman ba sa duba mu su a kan lokaci, ko kuma ma su cewa ba su da lokacin dubawa. To amma waɗannan abubuwa ne masu sauƙi, domin muddin kana son a duba maka aikin ka, to dole ka bayar da shi a lokaci, kuma ka rinƙa tuntuɓa cikin mutuntaka da girmamawa. Sannan shi kansa dillancin littattafan yana da alaƙa da kawo tasgaro wajen samar da wasu, domin akan fitar da su haka barkatai babu wani tsari ko wata ƙa’ida shimfiɗaɗɗiya. Amma da za a kawo wani tsari kwatankwacin yadda aka taɓa shimfiɗawa ga finafinan Haausa wajen shigar su kasuwa, to ina ganin za a sami farfaɗowarsu.

Idan mu ka koma baya, wajajen shekarar 2003 har zuwa 2007, akan fitar da finafinan Hausa barkatai babu wani tsari. Hakan sai ka ga fim ya shiga kasuwa ya gama cin kasuwarsa ba tare da an sani ba, balle a nema a kalla. Amma da suka bi wani tsari, a sati ake fitar da fim sau biyu, kuma a hakan ma, sai an bi layi, to sai abin ya sami armashi. To ina ganin irin wannan tsarin zai taimaka matuqa wajen farfaɗo da harkar rubuce-rubuce, hakan kuma zai sanya masanan su sami dammar bibiyar littattafan. Idan ban manta ba, a shekarar 2018, mun yi taron marubuta karo na biyu a Jihar Katsina, daga cikin bayanan da babban Malaminmu Farfesa Ibrahim Malumfashi ya mayar da hankali a kai, akwai yawaitar littatafan, kuma abin taƙaici sai ka gama karantawa; ba tare da ka fahimci ɗaya-ɗayar saƙo guda ba, wani kuma sai ka ga wani littafin aka sake kwaikwaya, ko kuma ka ga an gida littafin kan abubuwan da suka saɓa aladunmu da addininmu. Ina jin a shekarar 2019, na yi makamancin wannan bayani a wani taro da Hausa Authors Forum’ ta shirya a ɗakin taro na ‘American Space’ da ke Laburaren Murtala Muhammad Kano, duk da ni na fi karkatar da batun kan rashin tsari da bin dokokin rubutu ga marubutan online.

A taƙaice dai, baya ga rashin bin ƙaidoji da dokokin rubutun Hausa, akawai fitar su barkatai ba bisa tsari ba, akwai rashin kan-gado wajen kawo tasgaro ga littattafanmu na Hausa. A, ai ko yanzu akwai littattafan da mu ke sawa ɗalibai su yi nazari a kansu, kuma akan yi ayyukan bincike na kammala Difiloma, N.C.E, Digiri na ɗaya ko na biyu ko kuma na uku duk a kansu. Ni a karan-kaina, nakan sa ɗalibai sayen littattattafai domin mu nazarce su muddin an sami kwas ɗin da ya shafi haka, ko an sani gaɗar hakan. Misali, littafin ‘Tekun Labarai’ na Ɗanladi Z. Haruna, na sa ɗalibai sun saya mun yi nazarinsa a Jihar Yobe. A Kano kuwa, na sanya ɗalibai sun sayi littafin ‘Firgita Samari’ na Kabir Yusuf Anka. Sannan na bayar da ayyuka cikin wasu littattafai da dama, irin littattafan Fauziyya D. Suleiman da Maimuna Idris Beli, Bilkisu yusuf Ali da Ado Ahmad Gidan Dabino da wani littafi ‘Wuƙar Fawa’ ina jin na Hassana ko Maryam Kabir da dai sauransu masu yawa cikin wasu littattafan da suka dace mu karantar ko mu sa a yi nazari. Sannan ni da kaina, na yi nazarin wasu, ko a ƙarshen shekarar da ta gabata, ai na yi maƙala wadda na gabatar a taron ƙara wa juna sani wanda Jamiar Al-Ƙalam Katsina ta shirya, a kan littafin ‘Tuwon Ƙaya’, na Rahma Abdulmajid na yi, inda na fito da abubuwan da suka shafi Mazhabar Markisanci.

Ko za mu iya jin illolin da rashin bin ƙa’idojin rubutu ke kawo wa littafi da kuma marubucin?
Gaskiya ne, rashin bin ƙaidojin rubutu ga marubuci na da babbar illa, musamman daga ɓangaren mu ɗalibai da kuma malamai. Domin muddin idan aka ga marubuci ba ya kula da waxannan qaidoji, to daga lokacin za a daina karanta ko nazarin littafinsa a babi na ilimi, sai dai a xauka a karanta domin a kushe, ba don a yaba ba. Sannan rashin bin waxannan qaidojin yakan sanya a yi asarar ilimi mai yawa. Har wa yau, rashin bin qaida kan kasa gamsar da mai karatu, ko kuma a kasa fahimtar saqon da yake ciki, ko kuma ya jirkita saqon. Bari na ba da misali cikin wata maqala da na gabatar a shekarar 2018, a Jamiar Jihar Yobe. Ga wasu yan jimloli nan, waxanda suka sha bamban wajen rubutawa, muddin ba a bi qaida wajen rubuta su ba, to saqon zai bambanta. Idan ana son rubuta waxannan kalmomi da ke ƙasa:
Ba shi ya ci – Give him let him eat. 
Ya ƙi ya je – He refuse to go. 
Ta kai ya wuce – He passed through it. 
Kusato – Come close. 
Ka bari ya shiga – Let him enter. 
Da wa ya raba? – With whom he distributed? 
Sai ya rubuta su kamar haka:
Bashi ya ci – He was credited. 
Yaƙi ya je – He went for a war. 
Takai ya wuce – Takai has passed. 
Ku sato – Go and steal. 
Kabari ya shiga – He entered grave. 
Dawa ya raba – He distributed some corn. 

To, ko shakka babu ma’anar saƙon za ta sauya ne zuwa ga wata ma’anar da ba ita marubucin ke nufi ba, ko kuma ma a kasa samun ma’anar kwata-kwata. A taƙaice dai, rashin bin ƙaidojin rubutu kan kawo a ƙaurace wa littattafan marubuci, wanda hakan kan sanya a yi asarar ilimi da dama, sannan littafin da ba a bin ƙaidoji yana rasa kasuwa da makaranta.  

Malam, ana samun saɓani da bambancin ra’ayi wajen ƙa’idojin rubutu musamman wuraren haɗewa ko raba kalmar mallaka da abin mallaka, shin wace hanya kake ganin ya kamata a bi don samun daidaito ko yin amfani da ƙa’ida guda ɗaya?
Hanya mafi sauqi ta magance wannan matsala ita ce bitar abubuwan da suka wakana na tarukan da aka yi domin daidaita ƙa’idojin rubutun Hausa, sannan a tabbatar da matsaya a hukumance. Misali, an yi taruka da dama domin daidaita waɗannan ƙa’idoji da dokoki na rubutu, duk da gudu huɗu cikin tarukan su ne suka shahara, kuma ake jin su a bakunan mutane, waɗannan taruka sun haɗa da: 
i. Taron Bamako, 28 ga watan Fabrairu, zuwa 5 ga watan Maris, 1966. An yi shi a ƙarƙashin inuwar UNESCO.
ii. Taron Jamiar Ahmadu Bello, Zariya, 21 ga watan Yuni 1970.
iii. Taron Kwalejin Abdullahi Bayero Kano, watan Satumba, 1972.
iv. Taron Jamiar Yamai, 7-12 ga watan Janairu, 1980, wanda aka yi shi ƙarƙashin inuwar O.A.U.
Sai dai fa akwai tarukan da aka yi koma bayan waɗannan duk a kan ƙaidojin rubutu, misali akwai taron da aka yi a shekarar 1982, a ɗakin taro na Daula Hotel. Da taron da ‘Academy of African Languages’ (ACALAN) ta shirya a shekarar 2010 a Birnin Tarayya Abuja. Ko a shekarar da ta gabata, ina jin a watan Nuwamba, an yi taro kan waɗannan matsaloli na ƙaidojin rubutun Hausa a Jamiar Jihar Kaduna.

Abin da na ke so na ce a nan shi ne, muddin ana son magance waɗannan matsalolin, to sai an koma ga sakamakon waɗannan taruka, an yi bitar tattaunawar da aka yi, sannnan a sake bijiro da wasu abubuwan da ake ganin akwai buƙatar bijirowa, da kuma ƙoƙarin haɗe qaidojin rubutun Nijeriya da Jamhuriyar Nijar.

Ko za mu samu misalai na kalmomin haɗewa da rabewa da aka fi samun matsala kansu?
Galibi ire-iren waɗannan matsaloli an fi samun su a kalmomin mallaka ko nasaba. Amma idan da za a koma ga littafin babban malaminmu, Farfesa Bello Said na Jamiar Bayero, za a sami misalai da dama kan wannan batu, wato littafinsa mai suna Ƙa’idojin Rubutun Hausa: Jagora ga Marubuta. A littafin, ya yi ƙoƙarin tattauna ire-iren waɗannan matsaloli, musamman abin da ya shafi haɗe kalma ko rabawa. Misali, akan raba kalmomi a muhallan jakada wa, da harɗaɗɗun kalmomi, da lamirin suna/manunin lokaci na Lokaci na Gaba na 1, ko kalmomi masu gava ɗaya, ko wakilan sunaye da aikatau, da kalmomin dirka, da kuma kalmomin da kan zo tare da haɗuwar lamirin suna da aikatau mai gava ɗaya. Sannan a gefe guda kuwa, akan haɗe kalmomi a muhallan mallaka, wato idan mallakar gajera ce, domin ita doguwar mallaka ba a liƙa ta a jikin abin da aka mallaka, da muhallan da aka sami ɗafa ƙeya wa, da harɗaɗun sunaye (sai dai ana amfani da karan-ɗori a tsakaninsu), da kalmomin manuni/ishara, da kalmomin jamu, da haɗuwar wakilin suna da manunin lokaci, da wurin da aka sami haɗuwar ma da wakilin suna gajere da sauransu. Wannan kam, ni da Dr. Zainab Umar Saleh ma mun yi rubutu a kai, kuma littafin yana dab da shigowa kasuwa insha Allahu.

Wacce hanya ce marubuci zai bi don ganin ya inganta rubutunsa?
Na sha faɗa a taruka mabambanta cewa, muddin ana son inganta harkar rubutun Hausa, to fa sai an bayar da horo ga masu rubutun, maana marubutan, sannan su kansu masu buga musu a kwamfuyuta, suna buƙatar horo na musamman. Ina jin tun wajajen shekarar 2015, a taron da Duniyar Marubuta suka shirya ƙarƙashin jagorancin su Muhammad Lawal Barista da El-amin Daurawa a ɗakin taro na Hukumar Hizba da ke Unguwa Uku, cikin birnin Kano cewa; na fara wannan maganar. Ina da tabbacin idan an yi haka, ana bayar da wannan horo a kai a kai, tare da nuna wa lalle hakan tilas ne ga dukkanin marubuci, to za a sami daidaito, kuma waɗannan rubuce-rubuce za su inganta insha Allahu. Domin Malaminmu Farfesa Ibrahim Malumfashi ya taɓa wannan yunƙuri na bayar da horo ga marubuta, kai ba ma taɓi ba, har aji ya buɗe ma na a ‘Facebook’ domin bayar da horo, sannan ya yi alwashin yin hakan a zahiri.

Madallah. Mun gode da wannan dogon bayyani na ilimi.
Ni ma na gode ƙwarai. Wassalamu alaikum.